HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano
[ad_1]
Mariya Sanusi Dantata, mahaifiyar attajirin Afirka Aliko Dangote, tare da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, sun halarci gasar karatun Alƙur’ani da Maryam Shettima ta shirya a Jihar Kano.
An yi gasar laƙabi da #ReciteWithShetty, inda taken shi ne “Alƙur’ani: Jagora Wajen Tsaftace Kafofin Sada Zumunta”.
Manufar gasar ita ce bunƙasa tarbiyya da inganta amfani da kafafen sada zumunta.
A yayin karrama waɗanda suka shiga gasar, Shetty, ta bayyana cewa dubban yara daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka shiga gasar ta hanyar kafafen sada zumunta.
“Na yi mamakin yawan mahalarta. Hakan ya nuna akwai haziƙan matasa da dama a fadi5n ƙasar nan,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa gasar ba wai kawai ta nuna hazaƙar wajen karatun Alƙur’ani ba ce, face kafafen sada zumunta za su iya taimaka wa matasa wajen samun tarbiyya.
Wanda ya lashe gasar ya samu kyautar Naira miliyan ɗaya, yayin da na biyu da na uku suka tafi da kyaututtuka masu gwaɓi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link