Hisbah ta kama mutum 84 kan zargin aikata baɗala a Yobe
[ad_1]
Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe, ta kama mutane 84 bisa zargin aikata karuwanci da baɗala a Ƙaramar Hukumar Bursari.
Shugaban hukumar, Dakta Yahuza Hamza, ya tabbatar wa manema labarai kamen a Damaturu.
Ya ce an kama mutanen ne a wani samame da jami’an tsaron hukumar suka kai yankin Walawa, a garin Garin Alkali.
A cewarsa, “An kama maza 34 da mata 50 tare da kwalaben barasa da yawa.
“Haka kuma, an rufe duk gidajen da ake zargi suna aikata laifukan.”
Ya ƙara da cewa, an ƙwato barasa da yawa waɗanda suka cika manyan motoci huɗu.
Dakta Yahuza ya ce: “Waɗanda aka kama suna tsare yanzu, kuma za a kai su kotu kamar yadda doka ta tanada.”
Ya kuma gargaɗi sauran masu irin wannan hali da su daina, inda ya jaddada cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da yaƙar ɗabi’un da ke lalata tarbiyyar al’umma a Yobe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link