Haaland Ya Kafa Sabon Tarihin Jefa Ƙwallaye A Gasar Firimiya



Erling Haaland ya karya tarihin Alan Shearer ta hanyar zama dan wasan da yafi saurin cimma nasarar zura kwallaye 100 a gasar Firimiya fiye da kowa a tarihin gasar, inda ya kafa wannan tarihin a wasan da Manchester City ta doke Fulham da ci 5-4 a ranar Talata.

Dan wasan Norway mai shekaru 25, zuwa yanzu ya zura kwallaye 20 a wasanni 19 da ya bugawa Manchester City a dukkan gasa, Haaland ya shigo wasan na Fulham bayan buga wasanni uku a jere ba tareda ya zura kwallo ko daya ba, Haaland bai jefa kwallo ba a rashin nasara da Newcastle da Bayer Leverkusen sai kuma nasarar da suka samu a kan Leeds a karshen mako.

Erling Haaland ya rubuta sunansa a cikin littafin tarihin kwallon kafa na Ingila bayan ya karya tarihin zama dan wasa mafi sauri da ya ci kwallaye 100 a gasar Firimiya, dan wasan gaban Norway Haaland ya zama dan wasa na 35 da ya cimma wannan nasarar kuma na farko tun bayan Heung-Min Son a shekarar 2023, ya kuma share tarihin Alan Shearer wanda ya tsawon shekaru 30.

Tun lokacin da ya fara buga gasar Firimiya a kakar wasan 2022/23, Haaland ya zura kwallaye 10 a wasanni 6 na farko, Haaland ya zama dan wasa mafi sauri a tarihi da ya ci kwallaye 50 a gasar Firimiya, ” Ina alfahari da wannan tarihin kuma ina fatan cigaba da taimakawa Manchester City ta hanyar zura kwallaye masu muhimmanci” Haaland ya fadawa yan jarida bayan kammala wasan.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *