H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa

[ad_1]



Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa.

Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, kan yawaitar ambaliya a yankin.

A cewar Injiniya Bichi, “Mun karɓi kokenku hannu biyu. Matakin da shugabancin Jahun ya ɗauka ya yi dai-dai. Za mu tura ƙwararrun injiniyoyi su yi aikin da ya kamata domin daƙile ambaliyar, tare da inganta noman yankin ta hanyar gina madatsar ruwa domin ruwan sha da na aikin gona.”

A nasa bangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Jahun, Hon. Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, ya ce sun gabatar da koken ne saboda matsalar ambaliyar ta daɗe tana addabar su ba tare da samun mafita ba.

Ya ce, “Muna godiya bisa yadda kuka amsa kiranmu. Kun zo kun duba matattarar ruwan Akama da ta Fande tare da ƙwararrun injiniyoyinku. Wannan ya nuna ku na da niyyar magance matsalar da ta dade tana damunmu.”

Tawagar hukumar da ta kai ziyarar ta haɗa da Daraktan Kuɗi da Mulki, Musa Iliyasu Kwankwaso; Daraktan Tsare-tsare, Alhaji Tijjani Musa Isah; Daraktan Na’urori, Injiniya Dan Baffa Abdulƙadir; da Injiniya Sabi’u Ɗan Malan, tare da sauran manyan jami’an hukumar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *