Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Zulum Kan Faɗaɗa Ilimin Fasaha Da Sana’o’i A Borno
[ad_1]
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yabawa gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bisa ƙarfafa Ilimin Fasaha da Horon Sana’o’i a jihar, bayan kammala horar da kusan ɗalibai 3,000 daga cibiyoyin koyon sana’o’i guda tara da ke faɗin jihar.
Yabon ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, wadda Boriowo Folasade, Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ta sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, ya bayyana wannan shiri a matsayin babban mataki na ƙarfafa matasan Nijeriya ta hanyar ba su ƙwarewa masu amfani da za su iya samun aikin yi da su.
Ministan ya ce: “Wannan shiri da Gwamna Zulum ya ƙaddamar babban mataki ne na bai wa matasan Nijeriya ƙwarewa ta aiki da za su iya dogaro da ita wajen samun abin yi.”
[ad_2]
Source link