Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

[ad_1]


Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da iƙirarin Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya sake jaddada cewa ana yi wa Kirista kisan ƙare dangi a Nijeriya, tare da sanar da cewa ƙasar ta sake shiga cikin jerin ƙasashen da ake sanya wa ido saboda wannan zargi.

A cewar Trump, wanda ya yi wannan furuci ranar Juma’a, addinin Kirista yana fuskantar barazana ta ɓacewa daga Nijeriya saboda cin zarafi da kisa da ake yi wa mabiya addinin. Wannan matakin ya tunatar da abin da ya faru a watan Disamban 2020, lokacin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta saka Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake sanya wa ido kan keta haƙƙin ’yancin addini.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta fito daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, mai ɗauke da sa hannun kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa, gwamnati ta bayyana cewa ikirarin Trump “ba shi da tushe kuma ƙarya ce kawai.” Ta ce babu wani shaidar da ke nuna ana kisan kare dangi bisa bambancin addini a Nijeriya, inda ta ƙara da cewa ’yan ƙasa na addinai daban-daban suna rayuwa tare cikin lumana da fahimtar juna.

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da manufofi da ke kare haƙƙin ɗan adam da ’yancin addini, tare da ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a ƙasar.

Sanarwar ta ƙare da cewa Nijeriya za ta ci gaba da yaƙi da ta’addanci, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma gina dangantaka mai ƙarfi tsakanin mabiya addinai, domin tabbatar da ƙasa mai ɗorewa da fahimtar juna.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *