Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafa

[ad_1]



Bayan sama da shekaru biyu a kan mulki, gwamnatin Sakkwato ta fara waiwayar ’yan gudun hijira da hare-haren ’yan bindiga suka raba da muhallansu.

A dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar akwai ’yan gudun hijira da ke buƙatar ɗauki.

Wasu ma sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar, inda suka yada zango a jihohin Dosso, Maradi da Tahoua.

Mutane da dama, musamman yara, suna cikin mawuyacin hali.

Wasu marayu suna yin sana’o’i kamar tuƙa baro, tara dutse ko yin bara domin samun abin ci, ba tare da wata kulawa daga gwamnati ba.

Da yawa daga cikinsu ba sa zuwa makaranta saboda yunwa da rashin tallafi.

A ƙoƙarin samar wa waɗanda suka rasa ’yan uwa a hare-haren baya-bayan nan, gwamnatin Sakkwato ta raba tallafin Naira miliyan 69.75 da buhun shinkafa 210 ga iyalan waɗanda abin ya shafa a Kware da Gwadabawa.

Gwamna Ahmad Aliyu, ya bayyana hare-haren a matsayin abin baƙin ciki, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kuma kare al’ummar jihar.

Ya nuna damuwa kan yadda wasu ke bai wa ’yan bindiga bayanai, wanda hakan ke kawo rashin tsaro.

Dangane da rabon tallafin, gwamnati ta ce duk wanda ya rasa ɗan uwansa zai samu Naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar.

Waɗanda suka samu rauni za su karɓi Naira dubu 250 da buhunan shinkafa uku.

A Kware an kashe mutane 22, a Gwadabawa kuwa mutane 11 ne suka rasu, yayin da wasu 11 suka ji rauni.

Ana sa ran wannan tallafi zai zagaya sauran ƙananan hukumomin jihar, tare da ƙarin tallafi ga dubban ’yan gudun hijira da ke buƙatar taimako.

Ga hotunan yadda rabon tallafin ya gudana:


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *