Gwamnatin Kano ta ayyana hutu gobe Juma’a
[ad_1]
Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Juma’a, 12 ga watan Satumban 2025, wadda za ta yi daidai da 19 ga watan Rabi’ul Awwal na 1447, a matsayin ranar hutun Takutaha.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Salisu Mustapha, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun yana cikin girmama ranar bakwai ga haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
“Mutanen Kano sun shafe shekaru suna bikin wannan rana a matsayin Ranar Takutaha.
“Bikin Ranar Takutaha wani tsohon tarihi ne da aka shafe shekaru aru-aru ana gudanarwa.”
Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokacin domin yin tuntuntuni a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah Ya shiga al’amuranmu a wannan lokaci mawuyaci, Ya kuma ba mu albarkacin wannan damuna.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’ar makon jiya a matsayin ranar hutun Maulidi, domin bai wa Musulmi damar murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link