EFCC Ta Gurfanar Da Kwamishinan Kuɗi Na Bauchi Kan Zargin Badaƙalar Naira Biliyan 5.7
[ad_1]
Daga Khalid Idris Doya
Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) a ranar Talata ta gurfanar da Kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi kuma tsohon manajan reshen bankin Polaris a Bauchi, Yakubu Adamu, a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babban Kotun tarayya da ke Maitama, Abuja bisa zarginsa da hannu wajen badaƙalar kuɗaɗe har N5,791,900,000.
Adamu, an gurfanar da shi tare da kamfanin Ayab Agro Products da Freight Company Limited kan zarge-zargen guda shida da suka haɗa da sama da faɗi wanda ya saɓa wa sashi 21(a) da aka tanadar da hukunci bisa sashi 21 na dokar badaƙalar kuɗaɗe ta shekarar 2022.
- An Yi Taron Ayyukan Noma Na Kwamitin Tsakiyar Kasar Sin A Beijing
- Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki a Janairu 1, 2026 — Tinubu
A lokacin da aka fara shari’ar, Lauyan masu shigar da ƙara, Samuel I. Chime, ya shaida wa kotu sun gabatar da ƙarar ne tare da roƙon a ba su damar su karanta ma wanda ake zargin tuhumar da ake masa.
Bayan karanta masa tuhume-tuhumensa, Yakubu Adamu ya ƙi amsa dukkanin zarge-zargen.
Ɗaya daga cikin zargin da ake yi wa Adamu shi ne, a lokacin da yake matsayin manajan reshen bankin Polaris da ke Bauchi a tsakanin watan Yuni zuwa Disamban 2023, ya haɗa baki da Ishaku Mohammed Aliyu, manajan gudanarwa na kamfanin I.S. Makayye Investment Resources Limited, da Muntaka Mohammed Duguri, waɗanda dukkanninsu a halin yanzu ake nemansu wajen sama da faɗi da Naira biliyan 4.65.
A cewar tuhumar, ta bankin Polaris aka saki kuɗaɗen da nufin sayo Babura wa gwamnatin jihar Bauchi ta hannun kamfanin Emmanuel Asomugha General Enterprises, amma ba a aiwatar da kwangilar sayo Baburan ba.
Kazalika, a wani tuhumar kuma, an zargi Yakubu Adamu da cewa a wani lokaci a shekarar 2023 ya tura Naira miliyan 976 zuwa asusun ajiyar kamfanin I.S. Makayye Investment Resources Limited, tare da sanin kuɗaɗen sun fito ta haramtaccen hanya da ke da alaƙa da karkatar da kayan banki.
Bayan da shi Adamu ya musanta cewa bai aikata laifukan ba, mai gabatar da ƙara ya roƙi a tsare wanda ake zargin har zuwa lokacin da zai nemi beli. Sai dai Lauyan kariya, Gordy Uche, SAN, ya gabatar da buƙatar neman belin wanda yake karewa, yayin da Lauyan da ke shigar da kara ya ƙi amincewa.
Bayan sauraron muhawarar kowane ɓangare, Mai Shari’a Nwite ya ware ranar 2 ga watan Janairun 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da beli tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun EFCC.
[ad_2]
Source link