Category: Latest News

  • ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago

    [ad_1]



    Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa.

    A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnata kasuwanci da dukiyoyi ya jefa wasu iyalai da dama cikin ƙunci.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rushe kasuwar mai ɗimbin tarihi ya haifar da asarar kasuwanci da dukiyoyi, tare da kawo cikas ga hanyoyin rayuwar jama’a da haifar da matsaloli ga dubban mutane, ba a bayyana asarar rai ba.

    Kungiyar ta ACF ta jajanta wa waɗanda rusau ɗin ya rutsa da su, inda ta buƙace su dage wajen yin haƙurin lamarin.

    “Da fatan, waɗanda lamarin ya shafa za su kasance masu juriya masu ƙwazo, za su zo su taka rawa wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa su jure asarar da aka yi musu sanadin rushewar,” in ji Farfesa Muhammad-Baba.

    Kungiyar ta bayyana cewa tana neman ƙarin bayani kan lamarin don jawo hankalin gwamnatin Jihar Legas da kuma al’ummar da abin ya shafa don magance matsalar.

    A halin da ake ciki, ACF ta buƙaci gwamnati ta sa baki cikin gaggawa don taimaka wa waɗanda abin ya shafa.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da N32,000 A Matsayin Mafi Karancin Kuɗin Fansho

    [ad_1]

    Majalisar zartarwar jihar Bauchi (SEC) ta amince da fara biyan naira dubu 32 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin fansho na wata-wata ga tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar.

    Shugaban ma’aikatan jihar Bauchi (HoS), Barista Mohammed Sani Umar, shi ne ya sanar da amincewar yayin da ke shaida wa ‘yan jarida sakamakon zaman majalisar wanda ya gudana a jiya, ya bayyana cewar ƙarin ya biyo bayan amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi da gwamantin tarayya ta yi ne a baya.

    “Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta amince da fara aiwatar da sabon ƙarin mafi ƙarancin kuɗin da fansho daga Naira N12, 000 zuwa N32, 000, ƙarin wanda ya ma ya zarce N19, 000 ga tsofaffin ma’aikatanmu.

    “A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan.

    Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar.

    Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin daɗin tsofaffin ma’aikatan jihar, ya ce, karin zai kuma yi daidai da halin da tattalin arziki ya ke ciki a zahirance.

    “Tabbas ƙarin mafi ƙarancin kuɗin fansho zuwa Naira dubu talatin da biyu zai kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikatanmu da suka bayar da gudunmawarsu sosai wajen ci gaban jihar nan a lokacin da suke bakin aiki.

    “Gwamna ya nuna himma sosai wajen kyautata rayuwar ma’aikata da tsofaffin ma’aikata a jihar Bauchi. Yana fifita walwala da jin daɗinsu sosai,” Umar ya tabbatar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Kawo Wa Afirka Fatan Warware Matsalar Karancin Wutar Lantarki

    [ad_1]

    Kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya sun dade suna fama da matsalar karancin wutar lantarki, sai dai wani rahoto na baya-bayan nan da kungiyar Ember mai nazarin makamashi ta duniya ta fitar, ya nuna cewa wannan yanayi yana canzawa.

    Ta la’akari da yadda kasar Sin take samar da kaso 80% na allunan sola masu samar da wutar lantarki daga hasken rana na duniya, rahoton ya yi nazari a kan alkaluman shigar da allunan sola daga kasar Sin zuwa kasashen Afirka, tsakanin watan Yulin 2024 zuwa watan Yunin 2025, inda sakamako ya nuna cewa:

    1. Yawan allunan sola da aka shigar da su Afirka ya karu da kaso 60%;

    2. Karuwar shigar da allunan sola ta shafi kusan dukkan kasashen Afirka, inda jimillar wasu kasashe 20 a fannin ta kai matsayin koli a tarihi;

    3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka.

    Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci.

    Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na yanzu na dala 0.66 kan lita daya, man dizal na dala 60 zai samar da kWh 275 na wutar lantarki ne kawai. Wannan yana nufin cewa, ta hanyar amfani da allunan sola, kudin da aka yi tsiminsa zai biya kudin da aka kashe cikin watanni shida kacal. Ba a ma maganar saukin amfani, da damar biyan bukatar kare muhalli da allon ke da su.

    Sa’an nan, na san tabbas ana mamakin yadda allunan sola, da suka yi tsada a baya, suka yi araha a yanzu. Wannan ya faru ne saboda manufar kasar Sin ta bunkasa makamashi mai tsafta, ta kawo sauye-sauye ga yanayin kasuwar makamashi ta duniya.

    Tsakanin shekarar 2021 da ta 2025, kasar Sin ta gina tsarin amfani da makamashi da ake iya sabuntawa mafi girma da saurin ci gaba a duniya, wanda ya sa karfin kasar na samar da wutar lantarki ta makamashin da ake iya sabuntawa, ya karu daga kaso 40% zuwa kimanin kaso 60%. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta zama kasa ta farko wajen fitar da fasahohin makamashi mai tsafta a duniya, wadda take fitar da na’urorin samar da wutar lanarki daga hasken rana da iska zuwa kasashe da yankuna sama da 200. Ci gaban fasaha na kasar Sin da kuma karfinta na samar da dimbin kayayyaki cikin sauri sun tabbatar da rahusar kayayyakinta, da ba su damar samun karbuwa a tsakanin al’ummun kasashe daban daban. Bisa wani bincike da shafin yanar gizo na Carbon Brief da ke Burtaniya ya yi, cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta taimaka wajen rage matsakaicin kudin da ake kashewa domin samar da wutar lantarki daga hasken rana da kaso 80%.

    Albarkacin cudanya da kasuwanci da ake yi tsakanin Sin da Afirka, sannu a hankali sararin samaniyar Afirka na kara haskakawa da dare. Amma wannan mafari ne kawai. Saboda a bangare guda, nahiyar Afirka ce ke da kaso 40% na zafin hasken rana a duniya, da kaso 32% na karfin iska, da kaso 12% na karfin ruwa. A daya hannun kuma, neman ci gaban tattalin arziki da kare muhalli a lokaci guda, wani muhimmin jigo ne a hadin gwiwar Sin da Afirka. A cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta aiwatar da daruruwan ayyuka masu alaka da makamashi mai tsafta, da aikin raya tattalin arziki ta hanyar kare muhalli a Afirka. Ta hanyar musayar fasahohi, da hadin gwiwa kan wasu ayyuka, da samar da tallafi a bangaren hada-hadar kudi, kasar Sin na kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasashen Afirka a fannin raya makamashi mai tsafta. (Bello Wang)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara

    Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara

    [ad_1]



    Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar.

    Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal.

    Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro.

    Ya ce, tun daga shekarar 2013 Rotary ke gudanar da irin wannan shiri a sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya bayyana na Gombe a matsayin ta daban wanda aka gudanar a wurare biyu lokaci guda.

    Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ya yaba wa Rotary bisa haɗin gwiwa tare da kira ga jama’a su riƙa cin moriyar asibitocin da gwamnati ta sabunta a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

    Ya shawarci mata masu juna biyu da su riƙa zuwa duba lafiya a asibiti, kana iyaye su tabbatar da yin allurar rigakafi ga ‘ya’yansu ’yan ƙasa da shekara biyar domin kare su daga mutuwa marar dalili.

    Wasu daga cikin al’ummar da suka ci gajiyar shirin a Unguwar Kagarawal sun nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da abokan haɗin gwiwa bisa kawo musu tallafin jinya a kusa da su.


    [ad_2]

    Source link

  • Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi

    Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi

    [ad_1]

    Hukumar Ƴansanda a birnin Tripoli, Libya, ta kama wasu ƴan Nijeriya biyu bisa zargin hannu a wasu jerin fashin shagunan kasuwanci da ake gudanarwa a sassan birnin.

    Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a ranar 25 ga Agusta 2025, bayan wani bidiyon na’urar tsaro ya nuna su suna satar kaya daga wani shago. An ce dukkansu ba su da takardun izinin zama a ƙasar.

    Ƙungiyar Migrant ceton agogowadda ke sa ido kan al’amuran baƙi da ƴan gudun hijira a Libya, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata. Ta ce: “’Ƴansanda a Tripoli sun kama ƴan gudun hijira biyu daga Nijeriya bisa laifin shiga da kuma fashi a shagunan kasuwanci domin karɓe kuɗi. An miƙa su ga ofishin mai gabatar da ƙara.”

    Hukumomi sun yi imanin cewa waɗanda ake zargin na da alaƙa da wasu fasa shaguna da dama a cikin birnin, kuma yanzu haka an miƙa su ga mai gabatar da ƙara domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a kotu.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi

    An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi

    [ad_1]



    An kama wani Jami’in ɗan sanda bisa kashe wani soja a garin Futuk da ke Ƙaramar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

    Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji, 33 Artillery Brigade, Atang Hallet Solomon, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

    Ya ce, jami’in da ake zargin ya harbe sojan har lahira an kuma tsare shi, inda ya ce a halin yanzu ana gudanar da binciken haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sojoji.

    Hallet ya ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumomin tsaron biyu domin tabbatar da gudanar da cikakken bincike da kuma hana afkuwar lamarin nan gaba.

    Mafarauta da ’yan banga a garin Futuk sun ce lamarin ya biyo bayan cece-ku-ce tsakanin jami’an tsaro kan wata motar ɗaukar kaya da ake zargin na wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar China ne.

    Sun ce, motar da ke ɗauke da ma’adanai daga wurin haƙar ma’adinai na Yalo, an kama ta ne da yammacin ranar Litinin jim kaɗan bayan sallar Magariba.

    Shaidu sun ce sojojin na 33 Artillery Brigade da ke Bauchi sun umarci direban motar mai lamba Gombe 676 BLG da ya tsaya a wani shingen bincike da ke Futuk. Da direban ya ƙi amincewa, sai sojojin suka bi su suka tare motar a kusa da wata gada.

    Wani da ya buƙaci a sakaya sunansa kuma shaida ne ya ce, a yayin musayar yawu tsakanin sojan da aka harbe da wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.


    [ad_2]

    Source link

  • Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000

    Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000

    [ad_1]

    Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin yin Fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025.

    A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa wannan sabon tsari zai shafi aikace-aikacen da ake yi ne kawai a cikin Nijeriya.

    Sabon tsarin ya ƙayyade kuɗin fasfo na shafuka 32 mai ingancin shekaru biyar a kan N100,000, yayin da na shafuka 64 mai ingancin shekaru goma zai kasance N200,000. Sai dai an bayyana cewa kuɗin da ake biya ga ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba su sauya ba, inda ake cajin $150 ga shafuka 32 da $230 ga shafuka 64.

    Hukumar ta ce wannan mataki na da nufin kare inganci da sahihancin Fasfon Nijeriya tare da tabbatar da cewa ƴan ƙasa suna ci gaba da samun damar amfani da shi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Dangote Zai Gina Kamfanin Taki A Habasha Kan Dala Biliyan $2.5

    Dangote Zai Gina Kamfanin Taki A Habasha Kan Dala Biliyan $2.5

    [ad_1]

    Attajiri mafi kuɗi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Habasha domin gina masana’antar takin zamani mai darajar dala biliyan $2.5 a yankin Somali na gabashin ƙasar.

    An ƙulla yarjejeniyar ne a Addis Ababa ranar Alhamis, inda Dangote zai mallaki kaso 60% na aikin, yayin da Ethiopian Investment Holdings (EIH) za ta riƙe sauran kaso 40%. Bisa bayanan da aka fitar, aikin zai ɗauki watanni 40 kafin ya kammala, tare da samar da ton miliyan uku na taki a duk shekara. Ana haɗa masana’antar kai tsaye da iskar gas na Calub da Hilala da ke kudu maso gabashin Habasha, domin samar da kayayyaki.

    A cewar EIH, wannan aikin zai rage dogaro da shigo da taki daga waje, tare da rage matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta wajen samun kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje. Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da tsaron abinci a Habasha, yana mai cewa za ta samar da ayyukan yi da kuma wadataccen taki ga manoma.

    Dangote, wanda ke da masana’antar siminti a ƙasashe 10 na Afrika tare da cibiyar takin zamani mai samar da ton miliyan uku a Nijeriya, ya ce haɗin gwuiwar da aka cimma da Habasha na daga cikin muhimman matakai na tabbatar da burin Afrika na bunƙasa masana’antu da cimma isasshen abinci a nahiyar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ’Yan majalisar kasar Mexico sun yi naushe-naushe a zauren majalisa

    ’Yan majalisar kasar Mexico sun yi naushe-naushe a zauren majalisa

    [ad_1]



    ’Yan Majalisar Dattawan kasar Mexico sun yi naushe-naushe a ranar Laraba lokacin da muhawara ta yi zafi a zauren majalisar.

    Rahotanni sun ce an fara ba hammatar iska ne bayan shugabannin ’yan adawa a majalisar sun bukaci sojojin Amurka su shiga kasar su taya su yaki da dillalan miyagun kwayoyi.

    Shugaban marasa rinjaye a makalisar, Alejandro Moreno, shi ne dai ya je wajen yin jawabi a fusace bayan kammala zaman majalisar, inda ya tunkari shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona, saboda hana shi damar yin Magana.

    A cikin wani bidiyo a kafafen sada zumunta dai, an ga Alejandro yana tutture shugaban majalisar, yana dukansa a wuya, sannan ya bangaje wani wanda ya yi yunkurin shiga Tsakani a kasa.

    Rikicin dai ya biyo bayan zargin da aka yi wa jam’iyya mai mulki da ta adawa cewa suna goyon bayan shigar da sojojin Amurka cikin kasar, zargin da dukkan jam’iyyun suka karyata.

    Shugaban majalisar dai ya sha alwashin zai rubuta korafi a hukumance a kan dan majalisar da ya ci zarafin nasa, domin ya tabbatar da an hukunta shi t hanyar cire masa rigarsa ta kariya a matsayin dan majalisa.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000

    Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000

    [ad_1]



    Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025.

    A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne.

    “A yanzu duk fasfo mai shafi 32 ya koma N100,000 wanda zai yi shekara biyar kafin ya daina aiki, yayin da mai shafi 64 da zai shekara 10 ya koma N200,000,” in ji sanarwar.

    Sai dai sanarwar ta ce har yanzu kudaden da masu neman fasfo din daga kasashen waje ke biya na Dala 150 ga fasfo mai shafi 32 da Dala 230 a mai shafi 64, bai canza ba.

    Hukumar dai ta ce an yi karin ne domin a inganta inganci da tsaron fasfo din sannan kuma ya ci gaba da samuwa ga ’yan kasa.

    Yanzu haka dai kafin karin, ana biya N50,000 ga fasfo mai shafi 32, sai kuma N100,000 ga mai shafi 64.


    [ad_2]

    Source link