A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare.
Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen hada bayanai da fasahar kirkirarraiyar basira ta AI. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis.
Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya.
Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar da tan miliyan uku na takin zamani a kowace shekara.
“Wannan aikin zai samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa, ya tabbatar da wadatar takin zamani ga manomanmu da suka daɗe suna fama da ƙalubale.
“Sannan zai zama mataki na musamman a yunƙurinmu na cin gashin kai wajen samar da abinci,” in ji Abiy.
A watan Yuni, Aliko Dangote ya shaida cewa nahiyar Afirka za ta iya zama mai isar wa kanta da takin zamani cikin shekaru 40 bisa tsarin faɗaɗa masana’antarsa ta dala biliyan 2.5 da ke Legas.
A halin yanzu dai, Afirka na shigo da fiye da tan miliyan shida na takin zamani a kowace shekara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
AC Milan ta amince ta biya fam miliyan 36 domin siyan dan wasan gaban Chelsea, Christopher Nkunku yayin da Blues din ke dab da kulla yarjejeniya da dan wasan Manchester United Alejandro Garnacho, ana sa ran Nkunku, mai shekaru 27, zai rage yawan albashinsa domin ya koma kungiyar ta Italiya kan kwantiragin shekaru biyar, kuma an ba shi izinin tafiya don duba lafiyarsa.
Kungiyar ta Blues ta kuma hada da batun siyarwa wata kungiyar da ba ita ba a cikin kunshin kwantiragin, wanda zai kawo karshen zaman Nkunku na shekaru biyu a Stamford Bridge, rahoton ya ce matakin zai fi tasiri ga Chelsea, wadda yanzu haka take tattaunawa domin daukar Garnacho.
Dan wasan na Argentina, mai shekara 21, bai buga wa United wasa a kakar wasa ta bana ba, kuma yana daya daga cikin yan wasa da dama a kungiyar da suke atisaye a waje ba tareda rukunin kungiyar ba, har yanzu dai babu wata yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu, amma majiyoyi sun bayyana cewa an kusa kulla yarjejeniyar.
Siyar da Nkunku kuma yana nufin cewa Chelsea za ta iya samun riba a kasuwar musayar yan wasa, inda ka samu kusan fam miliyan 309 wajen siyar da yan wasa yayinda ta kashe fam miliyan 277 wajen sayen yan wasa, Nkunku ya zura kwallaye 18 sannan ya taimaka aka ci biyar a wasanni 62 da ya buga wa Chelsea, bayan ya koma Landan daga RB Leipzig kan fam miliyan 52 a shekarar 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Jagoran jam’iyyar NNPP a Nijeriya, Sanata Rabi’u Kwankwanso, ya ce suna jin daɗin jam’iyyarsu, kuma a halin da ake ciki babu wani ƙawance da suka ƙulla da wata jam’iyyar.
Yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar ƙoli na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, Sanata Kwankwaso ya ce ba gaggawa suke yi ba.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce kawo yanzu babu wata jam’iyya da suke tattaunawa da ita domin ƙulla ƙawance, sai dai ya ce hakan ba yana nufin ba za su tattauna da wata ba.
“’Yan jam’iyyarmu ba gaggawa suke yi ba, komai muna yinsa a hankali,” in ji shi.
“Muna da jam’iyyarmu (NNPP), kuma ba hanzari muke yi ba. Idan ana so a yi magana da mu babu matsala duk da ba mu manta da abin da aka yi mana a baya ba.
“Mu ’yan siyasa ne kuma a shirye muke mu tattauna da duk wanda ke son tattaunawa da mu.
“Har yanzu jam’iyyarmu na da rawar da za ta iya takawa a mulkin ƙasa,” in ji shi.
An dai jima ana raɗe-raɗin Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC, tun bayan zaɓen 2023, inda har aka riƙa hasashen ba shi minista, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya ce zai yi aiki da ’yan hamayya a gwamnatinsa.
Gwamnatin tarayya ta karrama Nafisa Abdullah Aminu, ‘yar shekara 17, daliba daga jihar Yobe, wacce ta zama ta daya a duniya a gasar ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan na kasar Birtaniya.
A wani bikin karramawa na musamman da aka yi a Abuja ranar Alhamis, Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suiwaba Sa’id Ahmad ne suka shirya bikin bajintar da Nafisa ta yi da sauran daliban da suka yi fice a gasar.
Sun bayyana ta a matsayin “wata fitacciyar tauraruwa wacce ta zama mai zaburarwa ga matasan Nijeriya.”
Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci.
Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Alhaji Sanusi Mikail Sami Gomo na III ya zama sabon Sarkin Zuru.
Kwamishinan Ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da hakan yau Alhamis, a fadar Sarkin Zuru wanda kuma ya miƙa masa takardar naɗin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya sanya wa hannu.
Ya ce, naɗin sabon Sarkin ya biyo bayan miƙa sunayen sarakuna uku da masarautar Zuru ta miƙa wa Gwamnan jihar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ƙara da cewa, Gwamnan wajen yin amfani da ikon da aka ba shi, ya amince da Alhaji Sanusi Mikail Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, wanda yanzu aka amince da shi a matsayin Gomo III.
Tun da farko, Sarkin Wasagu, Alhaji Muktari Musa wanda ya riƙe muƙamin muƙaddashin Sarki tun bayan rasuwar marigayin, ya karɓi baƙoncin sabon Sarkin a hukumance tare da maraba da dukkan baƙi a fadar.
A nasa jawabin, sabon Sarkin ya nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da kuma Gwamna Nasir Idris bisa amincewar da aka yi masa.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da aminci da kuma haɗin kai, yana mai ba su tabbacin buɗaɗɗiyar manufarsu da kuma jagoranci na bai ɗaya.
Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba.
Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma.
Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar.
Ambaliyar ta shafi wasu yankunan sassan Ƙananan hukumomin Lau da Karim_Lamido da Gassol da Ardo-kola
Gonakin da ambaliyar ta shafa sun haɗa da: Da na Shinkafa da Masara galibi da ke kusa da kogin Benuwe sun lalace yayin da gidaje da dama a ƙauyukan da ke gefen kogin Benuwe kuma suka nutse.
Alhaji Sale Binnari, a Ƙaramar hukumar Karim-Lamido ya shaida wa Daily Trust cewa ruwa ya lalata ɗaruruwan gonakin shinkafa da masara.
Garba Halilu, a garin Mutum-Biyu, Ƙaramar hukumar Gassol ya kuma shaida wa Daily Trust cewa, ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da dama a yankunan Mutum Biyu da yankin Kwatan Nanido da Maigemu da Sheka.
Ya ce, kogin ya malala a rassan gaɓarsa, sakamakon haka ɗaruruwan filayen noma ne suka nutse da ruwa.
Hakimin kauyen Sheka a Ƙaramar hukumar Gassol, Alhaji Haruna Sheka ya kuma ce gonaki da dama sun nutse da ruwa sakamakon ambaliya da ruwan kogin Benuwe.
A kokarin ganin an samu hadin Kai da zaman lafiya a yankin Arewacin Nijeriya, Kungiyar Samar da haɗin kai zaman lafiya domin ci gaba ta Arewa ( Arewa Cohesion For Peace Unity and Development Initiative) ta jaddada aniyarta na ganin yankin Arewa ya kara bunkasa ta bangarori daban-daban ta hanyar samar da zaman lafiya da hadin kan Al’ummar yankin.
Hakazalika, kungiyar ta kuma kaddamar da shugabannin kungiyar daga jihohi 20 na yankin Arewa da kuma kwanitocin da zasu jagorancin tafiyar da kungiyar.
Da yake Jawabi yayi kaddamar da shugabannin kungiyar Wanda ya gudana dakin taro na gidan Sardauna dake Jihar kaduna, darakta janar da kungiyar Dakta Abdullahi Idris, yace lokaci yayi da za’a samu hadin kai da zama lafiya a tsakanin alummar Arewa yana mai cewa kungiyarsu zata tabbatar da cewa ta bada nata gudummawar wajen ganin yankin Arewa ya kara bunkasa.
Yace sai da zaman lafiya da hadin ake samun ci gaba inda yace hakan ya sanya kungiyars ta dukufa wajen ganin an ceto yankin daga halin da yake ciki yanzu.
Dakta Abdullahi Idris, ya bukaci sabbin shugabannin da zage damtse wajen ganin an samu nasarar abinda suka sanya a gaba wajen samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa.
Akan hakan, ya bukace su da su zama jakadu na gari a jihohinsu wajen kare martabar kungiyar da kuma lalubo hanyar da za’a kara samun ci gaba a yankin Arewa baki daya.
A nasa jawabin, shugaban taron Alhaji Bature Umaru Masari, ya bayyana gamsuwarsa dangane da irin gudummawar kungiyar na hada kan alummar Arewa domin samun zaman lafiya.
Ya kuma bukaci sabbin shugabannin kungiyar dasu tabbatar da cewa sunyi aiki ba tare da nuna kabilanci kabila ko bambamcin addini ba Wanda hakan zai taimakawa kungiyar wajen ganin ta cimma burinta.
Darakta janar na kungiyar Dakta Abdullahi Idris, ya kuma rantsar da shugabannin kungiyar daga jihohi 20 da kuma kwamititoci uku da zasu tallafawa tafiyar da kungiyar.
An rantsar da tsohon shugaban kungiyar ‘yan Jarida ta kasa ( NUJ) reshen Jihar Kaduna Malam Garba Muhammad a matsayin shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da ayyukan saye-saye ta Sin ta gabatar da alkaluman jigilar kayayyaki a watanni 7 na farkon bana a yau, inda suka nuna cewa, jimillar kudaden jigilar kayayyaki a wadannan lokuta ta kai RMB yuan triliyan 201.9, wanda ke nuna cewa, an samu karuwar kashi 5.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Bukatun masana’antu a bangaren fasahar zamani da fannin rage hayaki mai gurbata muhalli sun samu karin ci gaba sosai.
A cikin wadannan watanni 7 na farkon bana, jimillar kudaden jigilar kayayyakin masana’antu ta karu da kashi 5.7 cikin dari. Bukatu a wannan bangare a fannoni 35 sun sami karuwa idan aka kwatanta da na bara, wato ya karu fiye da kashi 85 cikin dari. Daga cikinsu, bukatun masana’antu masu amfani da fasahar zamani na ci gaba da bunkasa cikin sauri.
Bukatun jigilar kayayyaki na yau da kullum sun ci gaba da karuwa tare da inganci. A cikin wadannan lokuta, jimillar kudaden jigilar kayayyakin yau da kullum ta karu da kashi 6.2 cikin dari, wadda ta fi ta rabin farkon shekara da kashi 0.1.
Kazalika, bukatu masu alaka da kayayyakin masarufi na ci gaba da farfadowa, yayin da manufar “maye tsoffin kaya da sabbi” ta haifar da matukar karuwar bukatun kayan lantarki da na’urorin bidiyo da sauti, da kuma kayan sadarwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Gwamnan Jihar kebbi, Dokta Nasir Idris Kauran Gwandu ya tabbatar da nadin Sanusi Mika’ilu Sami a Matsayin Sabon Sarkin Zuru, Wanda nadinsa ya biyo bayan rasuwar Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo II, Wanda ya rasu a ranar 16 ga watan Agusta 2025 a wata Asibiti dake kasar London.
Sanar wa nadin sabon Sarkin na zuru, ya fito ne daga bakin Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomi da Masarautun gargajiya na jihar, Alhaji Abubakar Garba Dutsinmari a yammacin Alhamisa din nan a garin na zuru.
Kwamishinan ya ce” nadin Sanusi Mika’ilu Sami bisa ga sakamakon zaben da rahoton da kwamitin tantance wa da zaben sarki na masarautar ta zuru, inda kwamitin suka tantance mutane uku kan mukamin sabon Sarkin Zuru.
Acikin mutun ukun da aka tantance Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami ya samu kuri’u mafi rinjaye a Matsayin Wanda aka zaba shi a zama sabon Sarkin na zuru. Bisa ga hakan ne Gwamnan Jihar ya sanya hannu kan hadin Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami a Matsayin Sabon Sarkin Zuru.
Dutsinmari ya gabatar da takardar nadin sabon Sarkin ga Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami, inda ya taya shi murnar zama sabon Sarkin Zuru.
Haka kuma ya godewa Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu kan nada Sanusi Mika’ilu Sami a Matsayin Sabon Sarkin Zuru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe