Tsohon ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya zargi Shugaba Bola Tinubu da watsi da jihar Zamfara duk da irin gudunmawar da ya bayar a zaɓen 2023.
Marafa, wanda shi ne ya jagoranci yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima a Zamfara, ya ce matakin da ya ɗauka ya biyo bayan taro na kwanaki biyu da ya yi da magoya bayansa a fadin jihar. Kungiyar ta bayyana cewa duk da nasarar Tinubu a Zamfara ƙarƙashin jagorancin Marafa, jihar ta ƙara fuskantar matsalar tsaro da kuma wariyar siyasa.
Kididdiga ta nuna cewa a shekarar 2024, Zamfara ce ta fi kowace jiha yawan sace-sacen mutane a Nijeriya, inda aka samu fiye da mutum 1,200 da aka yi garkuwa da su. Duk da haka, jihar ba ta samu komai daga gwamnatin Tarayya sai matsayin Ministan Jiha, alhali sauran jihohin Arewa maso Yamma sun samu ministoci biyu-biyu.
Kungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi da mazabu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi.
–
Wannan sigar za ta fi ja hankalin masu karatu a yanar gizo. Kana so in ƙara ƙaramin taken ƙasa (sub-headline) da ke ƙara jan hankali, irin na jaridu, misali: “Tsohon Sanatan Ya Ce Zamfara Ta Fi Kowa Fama da Sace-Sace Amma Gwamnati T
a Yi Watsi da Ita”?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Cutar tarin fuka (TB), na daya daga cikin cututtuka mafi muni da kuma dadewa a duniya, wadda take ci gaba da lakume rayukan dubun nan ‘yan Nijeriya a kowace shekara, duk da cewa; ana iya yin rigakafi, ana kuma warkewa.
A shekarar 2023 kadai, Nijeriya ta samu mutuwar mutum 71,000, wadanda ke dauke da wannan cuta ta tarin fuka, inda ta zama ta daya a Afirka, kuma ta shida a duniya cikin kasashen da ke fama da ita.
An samu sabbin wadanda suka kamu da wannan cuta ta TB, su kimanin 499,000 a 2023, wadanda ke wakiltar kusan kashi 20 cikin 100 na masu dauke da cutar a Afirka, sannan kuma kashi 18 cikin 100 na wadanda cutar ta kashe a nahiyar. Duk kuwa da cewa, ana samun magunguna da gwaje-gwaje na cutar kyauta a dukkanin fadin kasar, sannan akwai dubbai wadanda ba a auna su ba da kuma wadanda suka fara shan magani a makare, wannan na taimakawa wajen ci gaba da yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar.
Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi.
Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin fuka wanda ba ya jin magani, shi ne wanda ya fi illa. “Adadin yawan masu dauke da cutar da ba a gano ba, su ne ke ci gaba da yada ta”, in ji shi.
Domin cike gibin da ake samu, gwamnatin tarayya a kwanan nan ta kaddamar da sauye-sauyen ayyukan fasaha. Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya sanar da tura na’urorin gwaji (D-ray) na wayar hannu guda 400 a fadin jihohin Nijeriya 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
“Wadannan rukunin, wadanda kwararru a bangaren ke sarrafa su, suna ba mu damar gano alamun cututtukan tarin fukar da ba a gano ba,” in ji Pate.
Gwamnati ta kuma damar yin gwajin kwayoyin cikin sauri. Tsakanin 2012 zuwa 2024, yawan kwararrun injinan gwaje-gwajen da aka samu sun karu daga 32 zuwa 513. Haka zalika, adadin cibiyoyin kula da tarin fuka ya kusan ninki biyu daga 12,606 a 2019, zuwa kusan 23,000 a 2024, wanda ya mamaye sama da rabin dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar.
Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da ta hada kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni.
Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa.
Hakan dai ya biyo bayan bukatar da dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Sabon birni ta Kudu, Aminu Mustafa Boza, ya gabatar gaban majalisar kan bukatar tallafa wa yankunan da iftila’in ya shafa.
Boza a yayin zaman majalisar wanda mataimakin shugabanta, Alhaji Kabiru Ibrahim ya jagoranta ranar Alhamis, ya nemi ta jawo hankalin hukumomin da lamarin ya shafa kan halin da kauyukan suka ciki
Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan, Sani Gumbula ya ce ruwan ya yi musu barna sosai don haka akwai bukatar gwamnati ta kawo musu agajin gaggawa.
“Yanzu abin da nake fada maka gidajenmu da yawa sun rushe, gonaki sun nutse a ruwa sanadin wannan iftila’i, mun yi asara matuka, muna kira ga gwamnati ta yi abin da ya dace a kankanen lokaci, gaskiya muna cikin damuwa,” in ji Sani.
Shugabannin al’umma na ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da shugabannin ƴan bindiga da suka daɗe suna addabar yankin. An gudanar da wannan taro ne a dajin Wurma, ɗaya daga cikin wuraren da rikicin ya fi ƙamari, ƙarƙashin jagorancin Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, tare da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Babangida Abdullahi Kurfi.
A yayin taron, Hakimin Kurfi ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon babi ga al’ummar Kurfi, yana mai jaddada cewa an zaɓi hanyar zaman lafiya domin ci gaban yankin. Ya kuma shawarci shugabannin ƴan bindigar da su kafa shugabancin gargajiya a tsakaninsu domin tabbatar da ɗawainiya da gaskiya.
Shugabannin ƴan bindiga kamar su Alhaji Usman Kachalla Ruga, da Sani Muhindinge, da Yahaya Sani (Hayyu), da Alhaji Shu’aibu sun yi alƙawarin daina kisan mutane, satar shanu da garkuwa da mutane. Sun tabbatar da cewa manoma za su iya komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali tare da alƙawarin sako mutanen da suke tsare da su.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Abdullahi, ya bayyana farin cikinsa kan wannan mataki, yana mai cewa Kurfi ya shiga sabon zamani na ci gaba. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta gyara makarantu da asibitoci tare da tabbatar da adalci ga duk wasu da aka kama.
Wannan yarjejeniya ta sanya Kurfi ta zama ƙaramar hukumar ta biyar a Katsina da ta ƙulla sulhu da ƴan bindiga, bayan Jibia, da Batsari, da Safana da Danmusa, abin da ya haifar da sabon fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa zai dawo yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya soki gwamnatin tarayya kan ƙarin kuɗin fasfo da aka sanar cikin makon nan. Ya bayyana cewa wannan ƙarin ya nuna rashin la’akari da halin da talakawa ke ciki a yau.
A cewar Obi, sabon farashin fasfo na – ₦100,000 mai shafuka 32 da ₦200,000 mai shafuka 64 – ya fi sabon albashin ƙasa na ₦70,000, abin da ya ce bai dace ba da halin da ma’aikata ke ciki.
Ya zargi gwamnati da ƙara ƙaƙabawa jama’a ƙarin nauyi maimakon sauƙaƙa musu, musamman a lokacin da tattalin arziƙin ƙasa ke cikin matsala.
Obi ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba lamarin, yana mai cewa abin da al’umma ke buƙata a yanzu shi ne manufofin da za su rage wahala, ba ƙara tsawwala taɓarɓarewar rayuwa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
A ranar 26 ga watan Agustan 2023, kungiyar Zauren Hausa ta Nijeriya ta jagoranci gudanar da taron Ranar Hausa ta Duniya a Jihar Kano. Taron ya gudana ne a zauren taro na Hassan da ke cikin Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), da ke Jihar Kano.
Taron, wanda ya gudana karkashin jagorancin Farfesa Maryam Mansur Yola, mataimakiyar shugabar Kungiyar Zauren Hausa ta Kasa, ya tabo abubuwa da dama da suka shafi rayuwar Bahaushe da al’adunsa da kuma yanayin yadda yake a da da yanzu.
Kafin a fara gudanar da taron, Malam Abdullahi Baba Dantse ya gabatar da wasannin zaurance ga mahalarta taron, sannan ya kara bayani kan muhimmancin zaurance a harshen Hausa.
Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.”
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron.
Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin ace an kawo irin wannan taron wannan kwalejin. Kuma masu shirya wannan taron sun aminta tare da kawo wannan taron nan.”
Dakta Sunusi ya kara da cewa, Hausa harshe ne wanda ya bunkasa matukar gaske ta hanyar da ya yi nisan da ba za a iya cewa ga inda harshen ya tsaya ba.
Ya ci gaba da cewa ire-iren wadannan tarukan ne ke kara fito da muhimmancin harshen a idon duniya, da kuma ga wadanda suke ganin kamar harshen ba shi da amfani.
Ita kuwa Farfesa Maryam Mansur Yola jaddada muhimmancin wannan rana ta yi ga duk wani mai amfani da harshen Hausa.
Farfesa ta ce kamar yadda aka fara bikin jiya ta hanyar bayar da horo ga wadanda suke amfani da harshen musamman a ayyukansu, kamar ‘yan jarida da masu fassara da malaman makaranta, yau kuma za a gudanar da wassanni da kuma nuna wasu daga cikin al’adun Bahaushe.
Farfesa Maryam ta bayyana dalilin da ya sa aka zabi wannan rana don mayar da ita Ranar Hausa ta Duniya, sakamakon ranar ce da aka kirkiri haruffa masu lankwasa da suka hada da ‘d, ‘b, ‘k, da sauransu, wadanda ke matukar dada wa harshen armashi.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wajen taron, akwai Hon. Sulaiman Mukhtar Ishak, dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Madobi, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Ilimi na Majalisar Dokoki ta Jihar Kano. Ya jaddada tare da nuna muhimmancin wannan harshe.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alhaji Sama’ila Ammani Mai Zare da Alhaji Garba Gasash, da Shugabannin Sashen Koyar da Harshen Hausa na manyan makarantun gaba da sikandire na Jihar Kano, da dalibai da malamai daga ciki da wajen jihar.
Masu wake-wake da makada sun nishadantar da mahalarta taron tare da baje basirar da Allah ya ba su ta hanyar amfani da harshen don isar da sako ko kuma bunkasa harshen.
Daga karshen taron an gudanar da wasannin dambe da langa da kuma nuna wasu daga cikin sana’o’in da Malam Bahaushe ke alfahari da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa.
A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar.
Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida suka goce daga kan layin, sai kuma guda da ke daukar manyan mutane.
Wakilinmu da ya koma tashar jirgin ta Kubwa a ranar Alhamis, ya samu labarin cewa hukumar ta NRC ta bayar da aikin gyaran ne ga wani kamfanin ƙasar Sin wanda kuma ya fara aikin gyaran a ranar Laraba da ta gabata.
An dai kai taragu ukun ne zuwa babban tashar hukumar da ke yankin Idu a Abuja, a yayin da a ke saran ɗauko ragowar shidan da kuma injin jirgin a ranar ta Alhamis, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Bayanan sun ce ana sa ran a fara gyaran ɓangaren layin dogon a ranar ta Alhamis bayan an kawar da ragowan taragun shida da a cewar majiyar ba za su iya tafiya da kansu ba har sai an ɗaga su a sakamakon lalacewar da suka yi.
A wani labarin kuma, yawancin ma’aikata da ke aiki a tashar jirgin ƙasan ta Kubwa, da sauran masu gudanar da ayyuka a wajen na ci gaba da hutun dole, lamarin da ya mayar da wajen tamkar na yanayin zaman makoki.
Wasu daga cikin ma’aikata ’yan ƙalilan da su ka leƙa wurin aiki a ranar, sun shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya fi shafar ma’aikata da ke ɓangaren sayar da tikitin jirgi, da masu aikin tsaftace wajen, da masu yin dako, sai kuma direbobin tasi, da dai sauransu.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka zanta da shi ya koka a kan yadda lamarin inda ya ce ya raba su da sana’arsu da kuma jefa su a cikin halin kunci.
Wata da ke aiki da kamfanin samar da abincin maƙulashe da ke raba dafaffiyar taliyar ga fasinjoji kyauta a duk ranakun Alhamis da Juma’a da kuma Asabar, ta ce ta je wajen a ranan tare da cikakken fatan an fara aiki.
Jami’ar mai suna Joy Ene Agu ta ce suna raba taliyar ne kamar katan huɗu a kowane yini cikin ranakun a matsayin dabarun tallata taliyarsu ga jama’a, sannan su sayar da ɗanyarta ga masu sha’awa a wajen don yin tsaraba.
Sai dai ta ce a yanzu sun rasa dukkanin abubuwan biyu, inda ta ɗauko tukunyarsu ta girkin da kuma kaskon gas ɗin da suke amfani da shi a wajen, ta bar tashar.
Taron ranar hausa ta duniya taro da majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 26 ga watan Agusta domin raya ta a duk fadin duniya.
To, sai a wannan karon taron ya sam u tagomashi inda masarautar Daura hadin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina suka shirya shi domin bunkasa harshen Hausa da kuma Hausawa.
Taken taron na wannan shekara ta 2025 shi ne “yin amfani da harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiya” kamar yadda aka bayyana tun kafin wannan rana.
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.
Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.
Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa.
Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta duniya.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan sun hada da gwamnan mulkin Soji na jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci ya jagoranta tare da mai martaba Sarkin Damagaram Sultan Abubakar Umar Sanda
An fara bude taron addu’a sannan fara baje kolin al’adu da sana’o’in Hausawa inda aka fara shakatawa da wanzamai bayan sun nuna ta so bajintar da kwanji da kuma makera wadanda suka yi wasan wuta a gaban dubun dubatar jama’ar da suka halarci taron.
Kazalika an yi wasan kokawa wanda shi ne ya kayayar da mahalarta taron, inda daga bisani aka shirya gagarumar daba ta hawan dawakai da ‘yan tauri da masu algaita da sauran su.
An shirya hawan dabar ne tamkar yadda masarautar Daura take shirya hawan Sallah ko Sallar Gani inda aka jero garuruwan Hausa bakwai da kuma kanne bakwai (tsohuwar banza bakwai)
Bayan kammala wannan daba da nuna al’adun gargajiya na bahaushe da hausawa an gudanar da jawabai daga manyan baki da suka halarci wannan taro na habaka harshen Hausa.
Sanata Ibrahim Ida Wazirin Katsina na daga cikin wadanda suka yi jawabi inda ya fara nuna mahimmancin da Majalisar dinkin Duniya ta baiwa harshen Hausa, al’adu da kuma adabin Hausawa a idun duniya.
Wazirin Katsina ya cigaba da bayanin cewa abu ne mai mahimmanci a fahimci cewa harshen Hausa na daga cikin manyan harsuna da ake amfani da su wajen magana, da sauran mu’amula ta yau da kullum.
Sanata Ibrahim Ida ya bayyana cewa yanzu an tabbatar da cewa harshen Hausa ya fi kowane harshe a Afrika yawan masu yin magana da shi da kuma yin huldodin rayuwa na yau da kullum.
Abdul Baki Jari na daya daga cikin wadanda suka assasa wannan rana ta ranar Hausa ta duniya wanda majalisar dinkin duniya ta amince a shekarar 2015.
Ya kara da cewa babban makasudin wannan taro shine domin a sada zumunci a tsakanin Hausawa da ke kasashe fiye da 25 a fadin duniya inda yanzu haka ana cigaba da irin wadannan bukukuwa.
Abdul Baki Jari ya nuna bukatar da ake da ita wajen gudanar da bincike akan makomar harshen Hausa da ke fuskantar kalubale a wasu kasashe.
Haka kuma ya nuna godiya da farin ciki da kasashe da suka halarci wannan taro musamman kasashen Camerou da Chadi da Ghana da Barkina Faso da sauran kasashen duniya wadanda aka ke tara ruwa kafin azo nan.
Shima da yake nasa jawabi wakilin shugaban kasar jamhuriyar Nijar kuma gwamnan jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci ya nuna godiya da fatan ga wadanda suka shirya wannan taro.
Kanal Massallaci ya bayyana cewa irin wadannan tarurruka shugaban kasar Nijar Janar Abdurrahaman Tiachni ke bukata domin ganin an hada kan hausawa wuri guda.
“Ya zama wajibi Hausawa su farka daga dogon barcin da suka yi, idan aka duba yanzu Hausawa sun fara barin gadon su, to ya zama dole a koma ma gado da al’adu irin wannan aka hada Iyaye da kakanni” in ji shi
Gwamnan Damagaram din ya yi fatan ya a rika amfani da irin wadannan tarurruka nan gaba domin kara dankon zumunci tsakanin kasashen Afrika inda nan ne Hausawa suka fi yawa.
Daga wadanda suka halarci wannan taro sun hada da gwamnan jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci da Mai martaba Sarkin Damagaram Sultan Abubakar Umar Sanda da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida da Sardaunan Kasar Hausa Mai tuta Hon. Alasan Ado Doguwa.
Sauran sun hada da wakilin gwamnan jihar Katsina kuma mai baiwa gwamna shawara akan harkokin masarautu Alhaji Usman Abba Jaye da sauran masu rike da masarautar da hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Sa’oi 24 da Fadar Shugaban kasa ta bigi ikirarin cewa, ofishin Malam Nuhu Ribadu a watanni 24 da suka gaba, ya samu nasara kan yakin da ke yi da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindigan Daji, kwatsam, sai kuma a makwannin da suka wuce, wasu mahara suka kutsa cikin wani Masallaci a garin Malumfashi na jihar Katsina suka kai mummunan hari a yayin da masallatan ke kan tsakiya da gabatar da Sallar Asuba, suka hallaka masallata 30.
Sai dai, abin da ake cewa wai, ihu bayan hari, daga baya jami’an tsaro a garin sun nemi daukin sauran jami’an tsaro domin kai dduki bayan maharan sun kaddamar da harin na su.
Fadar Gwamnatin kasa ta yi ikirarin cewa, Gwamnatin kasar ta gaji matsalar tsaron ne, daga Gwamnatin baya, amma ta yi ikirarin cewa, bisa dabarun da Nuhu ya samar, musamman ta hanyar yi wa tsarin tsaron kasar garambawul, da kuma yin aikin hadaka da sauran hukumomin tsaro, hakan ya sanya ofishin na Nuhu, samun nasara a wanzar da ayyukan tsaro na sirri, tare da kuma yin hadaka da hukumomin tsaro na kasa da kasa, musamman domin a kara karfafa tsaro a cikin kasa.
Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba.
Tabbas, muna jinjina masa kan yunkurin da yake ci gaba da yi na rage kalubalen rashin tsaro da Gwamnatin mai ci ta gada.
Amma mummunan harin da wasu mahara suka kai a watannin baya a yankin Yelwata, inda suka yi wa wasu al’umomin yankin kisan kiyashi da kuma harin da ‘yan bindiga suka kai kan Masallaci a garin Malumfashi ta Jihar Katsina, ba makawa hakan ya nuna cewa, kamar an yi gaggawa kan ga murnar samun nasara ta yakin da ofishin Nuhu ke kan yi, da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga Daji duk da kuwa nasarar kame da kuma kashe wasu kasurguman ‘yan ta’adda da ofishinsa ya yi.
Kazalika, irin wannan salon ikirarin samun nasara a yakin da ‘yan ta’adda ne, Gwamnatin da ta shude ta rinka shelanata cewa, ta samu, amma a zari, batun akwai lauje a cikin nadi.
Domin kuwa, kusan shekaru takwas na Gwamnatin da ta gabata ta yi, kalubalen rashin tsaro ya jefa rayuwarsu, a cikin tasku, duba da yadda ‘yan tayar da kayan baya a kasar suka kusan durkusar da bangaren tsaron kasar, ta hanyar aikata ayyukansu na ta’addacin wanda lamarin ya kai ga har an nuna bukatar a yi wa fannin tsaron garanbawul.
Bugu da kari, ‘yan Nijeriya da dama,, sun ta yin kiraye-kirayen da a dauki mataki kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar a zahirance, ba wai kawai yin bayanai, da fatar biki da hukumomin tsaron kasar ke yi na cewa, sun kurmushe kaifin ‘yan ta’addar Kungiyar Boko Haram.
Hakazalika, a tsakanin wadannan watannin, manyan hukumomin tsaro na kasa sun ta yin bayanan zaurance domin nunawa ‘yan kasa tamkar komai na tafiya daidai, bayan alhali a bayan fage, ‘yan ta’adda na ta kai komon, yunkurin durkusar da kasa.
Har zuwa yanzu, ‘yan Nijeriya na ci gaba da zama a cikin kwankwaton ikirarin da hukumomin tsaron kasar ke yi na murkushe kaifin ‘yan Boko Haram inda kuma a zahirance, ake ganin ‘yan gudun hijira a yankin Arewa Maso Gabas ke kara kwarara zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke a yankin domin tsira da rayuwarsu.
A gefe daya kuma, manyan hanyoyin kasar sun koma tamar tarkon mutuwa ga matafiya inda ake tare su, a wasu yankuna, a hall aka su.
Masu garkuwa da mutane da sauransu, na ci gaba hana ‘yan Nijeriya sakat saboda ayyukansu da suke ci gaba da gudanarwa.
An dai nada Nuhu Ribadu a mukamin mai bai wa shugaban kasa shawara ne, bisa la’akari da nasarorin da ya samar, a lokacin da ya kasance shi ne shugaba na farko, na hukumar EFCC.
Nuhu tsohon Dansanda ne, wanda ya yi ritaya, a matsayin mataikin Sifeta Janar na ‘Yan Sanda.
Amma idan har zamu yiwa hukumomin tsaron adalaci, za mu iya cewa sun yi kokar wajen kashe ‘yanbindiga da dakile hare-haren ‘yan ta’adda a jihohohi kamar Zamfara, Katsina, Kaduna da Sokoto.
Sai dai, bisa maganar gaskiya, har yanzu za a iya cewa, akwai sauran gagarumin jan aiki, a gaba, game da magance matsalolin rashin tsaro a kasa.
Kalubalen rashin tsaro da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da fuskanta matsala ce da ke bukatar yin tunani mai zurfi da bunkasa salon dabarun yaki tare da daukar kwararan matakan da suka kamata, domin a kawo karshenta.
Kamata ya a ce, ofishin Nuhu Ribadu ya zama tamkar cibiyar da za a zauna a wasa kwakwalwar yin nazarin tsara yadda za a tunkari kalubalen rashin tsaron musamman duba da cewa, zuwa kai farmaki fagen daga ba hurumin sa ba ne.
Malam Nuhu Ribadu na da bukatar samun kwararru da za su taimaka masa da kuma shi kan shi tsarin tsaron kasa.
Bugu da kari, batun na samun nasara a yakar ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga, ba shi ne abin da a yanzu ‘yan kasa ke bukatar ji ba, domin a namu ra’ayin abin da suke bukata daga gun hukumomin tsaron shi ne, kara jajircewarsu wajen samar da dawamamen zaman lafiya a kasa.
Muna kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya yi amfani da karfin ofishinsa wajen kara matsawa dakarun soji da ke a fagen daga na su kara kwazo kan yakin da suke ci gaba da yi da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga.
A namu ra’ayin, nuna ganin kamar an yi riga Malam Masallaci kan batun cewa, an samu nasara kan yakar ‘yan tayar da kayar baya a kasar nan, musamman duba da cewa, har yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da zama a cikin fargabar hare-haren’yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda.
Kazalika, duba da cewa, masallata a Masallatai na gudanar da ibada a cikin jimanin tsoro, wannan babban abin nuna damuwar ne bayan cewar, nauyi ne a kan jami’an tsaro su tabbatar da suna kare rayuka da dukokiyoyin ‘yan kasar .
Rashin imanin da ya aku a jihar Katsina da kuma a yankin Yelwata abune da ya nuna irin gazawar da ake da ita, bangaren samun bayanan sirri. A yayin da muke taya Fadar Shugaban kasa murnat samun wannan nasarar ,amma muna ganin har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba kan batun kalubalen rashin tsaro a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Annabi Muhammad (SAW) jinkai ne ga halitta baki daya saboda fadin Ubangiji, “wa ma arsalnaka illa rahmatan lil alamin – ba a aiko ka ba sai don ka zama rahama ga halitta”. Ya tabbata a hadisai ingantattu cewa, Manzon Allah (SAW), shi ne mai ceton halitta ranar Alkiyama, kamar yadda Alkur’ani ya tabbatar da fadinsa, “Asa an yab’asaka rabbuka makaman Mahmuda”.
Annabi (SAW), shi ne shugaban ‘ya’yan Annabi Adamu duka. Tun daga kan Annabi Adam zuwa na karshen ‘ya’yansa, duka za su kasance a karkashin tutar shugabancin Annabi (SAW) a ranar Alkiyama.
Annabi (SAW) shi ne cikamakon Annabawa kuma jagoransu, komai ya zo da shi, babu wani abu sabo da za a zo da shi, sai dai na Annabi (SAW) ne za a yi ta warware wa. Ko dai ya warware mana wata mas’ala da ba a fahimce ta ba ko kuma ya zo da wata sabuwar fahimta amma dai tana cikin abin da Annabi (SAW) ya zo da shi. Ita ce wannan ilimin kimiyya da fasaha da muke gani yanzun.
Addinin Annabi (SAW) shi ne mafificin Addinatai, duk da cewa sauran addinatan daga Ubangiji suke, amma ba kamar nasa. Al’ummar Annabi (SAW) ita ce mafificiyar al’umma. Babu yadda za a yi wannan al’umma ta zama mafificiyar al’umma amma annabinta bai zama mafificin Annabawa ba.
Littafin Manzon Allah (SAW) Alkur’ani, shi ne mafificin Littattafai, ya kunso Ilimai da sanin Allah. Shehu Ibrahim Inyass (RA), ya ce “Alkur’ani ya yi maganar kowanne fanni, duk wani dan fanni ya dauki maganar fanninsa a cikin Alkur’ani. Alkur’ani ba waka ba ne, wanda ya kawo shi ba mawaki ba ne, amma Larabci ne. Kowane harshe, yana da wake, amma Larabawa sun yi wake da yawa, don haka, akwai gurbinta a Alkur’ani.
Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita.
Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam da shi ba. Ya daukaka ambatonsa, ta inda ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW). Indai an kira sunan Allah, sai an kira sunan Annabinsa.
Allah ya yi masa budi (Fatahi) na Zahiri – Sulhu a Hudaibiyya, Fat’hu Khaibara, da Fat’hu Makkah; da Badini – Fatahi a Sifa, Fatahi a Suna da Fatahi a Zati.
Allah ya gafarta wa Manzon Allah (SAW), ya tafiyar da dauda ga ‘ya’yan gidansa, ya yi Isra’i da shi, ya rantse da zamaninsa da garin da aka haife shi, ya ba shi alkairi mai yawa (Alkausar), sannan kuma mu’ujizarsa ta wanzu har tashin alkiyama. Zamaninsa yana kara tsawo mu’ujizarsa tana kara fitowa amma sauran Annabawa, akasin haka ne.
Allah ya aiko Manzon Allah (SAW) zuwa ga halitta baki daya, Annabin duka nahiyoyin duniya ne.
Ya zo a cikin maganar waliyyai na abin da suka fada dangane da bambancin Annabi (SAW) a matsayin “Habibullahi” da Annabi Ibrahim AS a matsayin “Kalilullahi”: mukamin Annabi Ibrahim shi ne kwadayin gafara, saboda jirwaye mai kamar wanka da ya yi kan wata waki’a biyu da ta faru da shi; 1. Ya sare gumaka, ya ce a tambayi babbansu 2. Ya kira matarsa, Saratu da cewa ‘yar uwarsa ce.
Amma a bangaren Annabi (SAW), Ubangiji bai fadi laifin ba sai dai hukuncin kawai, da cewa, “mu muka yi maka budi, budi mabayyani, don mu yafe maka laifinka da wanda ka yi, da wanda za ka yi gaba…”, Abun nufi a nan, ittifakan Allah ya gafarta wa Annabi Ibrahim (AS) amma gafarar da aka yi wa Annabi (SAW), sai da aka hado ta da Gara – budi bayyananne, da gafarar abin da ya gabata da wanda zai zo a nan gaba, cika ni’imarsa a kan Habibinsa, shiriya kan tafarki madaidaici, da taimakon nasara mabuwayiya. Babu yadda za a yi wanda ke neman gafara ya yi daidai da wanda aka hado shi da irin wannan Gara.
Annabi Ibrahim ya roki Allah kar ya tozartar da shi ranar Alkiyama, amma shi Annabi (SAW), Ubangiji bai bayyana inda ya roka ba duk da cewa yana roko, sai ga shi Ubangiji ya sanya wa ranar Alkiyama suna da “ranar da Allah ba zai tozartar da Annabi (SAW) da wadanda suka yi imani da shi ba.” Alhamdulillah… duk wanda ya yi imani da Annabi (SAW), ya tsira. Duk wannan ukuba da ake ruwaitowa ta ranar Alkiyama, ba wanda yace karya ne amma wanda ya amsa Darikar Shehu Tijjani (Abul Abbas), sai dai ya farka a Aljannah ya ji duk an gama komai, wata kila aka ce Shehu ina hujjar fadin wannan, sai ya ce, Hadisi ya zo, ranar Alkiyama Umar zai amsa littafinsa na Shari’a da hannun dama, sai aka ce, ina Abubakar fa, aka ce yana cikin Aljannah lokacin.
Annabi Ibrahim (AS) ya roki Allah ya sa a yi ta yabonsa, ana fadin aikin alkairinsa har tashin Alkiyama, kuma Allah ya amsa masa wannan. Duk addinatai suna iya fadan batanci a kan wasu Annabawa amma Annabi Ibrahim duk addinatai suna yabonsa, kowa cewa yake nashi ne, sabida wannan addu’a (waj alliy lisana sidkin fil akhirin). Amma Annabi (SAW), ba a fada inda ya roka ba, sai ga shi Ubangiji yana ce masa (wa rafa’ana laka zikraka) mu muka daukaka ambatonka. Annabi (SAW) ya ce, ya Jibrilu mece ce fassarar haka? Ya ce, ban sani ba amma bari in tambaya, Jibrilu ya dawo da amsar cewa, Ubangijinka na nufin, duk in an ambace shi, sai an ambace ka. To yanzu ne aka yi zikiri. Ina masu da’awar Akida? Masu shirin sai sun kawar da ambaton Annabi (SAW), to Sahabbai dai sun gane! A yayin da ake yakin zubar da jini, ana sare wuya amma Annabi suke kira (ya Muhammada) kuma ba su yi shirka ba. A ko ina aka ambaci Ubangiji sai an ambaci Annabinsa (SAW). A wasu wurare ma da yawa a Alkur’ani Allah ya hade sunansa da Annabinsa (SAW), “wallahu wa rasuluhu a hakku an yurduhu – da Allah da Annabinsa, shi yafi cancanta a yarda da shi”.
Annabi Ibrahim ya yi addu’ar cewa, Ubangiji ya tsare shi da zuriyarsa daga bautar gunki, wanda ake bautama wa, amma ‘yar tsana, ko zanen sarakuna ko na mazan jiya da ake zanawa don jinjina ba don bauta ba, wannan ba sunan shi gunki ba. Annabi Ibrahim yana nufin zuriyarsa ta bar bautar Ubangiji ta koma ta Gumaka, Allah ya tsare su. Kuma Allah ya yi masa haka.
Da wannan, wasu Malamai suka kafa hujjar cewa, iyayen Annabi (SAW), suna kan addinin Annabi Ibrahim (Hanafi).
Annabi Ibrahim ya roki Ubangiji ya tsare shi da zuriyarsa daga bautar gunki amma Annabi (SAW), Allah ne ya tafiyar da kazanta daga zuriyarsa da ke cikin bargo gaba daya ba bautar gunki kadai bai.
Mece ce kazanta (Rijsu)? Giya da caca da bautar gumaka, da kuma rantsuwa da gumaka. Sannan kuma, ya tsarkake su tsarkakewa. Don haka, yadda dan Adam ba zai iya tashi sama ba, haka zuriyar Annabi (SAW) ba za ta iya sabo ba. Da wannan za mu fada cewa, Annabi Ibrahim ya roki abu daya, amma Annabi (SAW) sai da aka bashi hudu.
Fadakarwa game da cikar Manzon Allah (SAW) shekara 1,500 da haihuwa
Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, Allah ya kawo mu watan Rabi’ul Auwal, maulidin da za a yi na ranar 12 ga watan shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci, zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1447 ta bana, lissafin zai ba ka cewa Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1500 da haihuwa.
Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu da Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal na bana, lokacin da Manzon Allah ya cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu da zai kara wasu shekaru 500 a raye.
A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe