’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa.
Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda.
An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata.
A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su.
Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kira ɗan uwan Halimat, Malam Ibrahim, ta wayar Anas domin neman kudin fansa Naira Miliyan 600.
Sai dai iyalan sun bayyana cewa ba za su iya biyan wannan kuɗi ba.
Radda ya dawo daga hutu saboda hare-haren ’yan bindiga a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya dawo daga hutun jinyar da yake yi a ƙasashen waje, sakamakon sabbin hare-haren ’yan bindiga a jihar.
A ranar Laraba, gwamnan ya kai ziyara ta’aziyya ƙauyen Gidan Mantau, a Karamar Hukumar Malumfashi, inda ’yan bindiga suka kashe masallata a wani masallaci a ranar 19 ga watan Agusta.
Shaidu sun ce harin ya auku ne a lokacin da jama’a ke yin sallar Asuba.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, bayan da mutanen yankin suka yi musu kwanton-ɓauna, tare da kashe mutanensu sannan suka ƙwace musu makamai da babura.
Hakazalika, an ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙone sama da mutum 20 a gidajensu lokacin da suka sake kai hari Gidan Adamu Mantau, a Unguwar Yar Mai Dabo, Makera da kuma Burdigau.
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni.
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC.
El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba.
“Ba abin da wannan gwamnatin ke yi ban da karya a kullu-yaumin. Kowa ya san gaskiya. Ni ba na neman kowacce irin kujera. Ba zan tsaya takarar Sanata ba ko ma kowanne irin matsayi, shi ya sa nake rokonku da ku zo mu hada hannu mu kori azzalumai,” in ji shi.
Ya ce a baya abin da ya tsara shi ne bayan ya sauka daga Gwamna zai yi ritaya daga harkokin siyasa gaba daya, amma abubuwan da ke faruwa ne suka tailasta masa dawowa, kodayake babu bukatar kashin kansa a ciki.
Tsohon Gwamnan ya ce burinsa shi ne ya taimaki matasa da mata da masu rajin kawo ci gaba domin su karbe ragamar siyasa su kawo canjin da ake bukata.
Daga nan sai ya bukaci mutane da su je su yi rajistar zaben da aka fara domin shiga harkokin zabe ka’in da na’in.
A halin yanzu a duk fadin kasar Sin, ana samun wani irin sabon sauyi kan abin da ya shafi kyautata walwalar rayuwar yau da kullum ta miliyoyin jama’a, inda gwamnatocin manyan birane ke bude hanyoyin kashe kudi da ciniki a bangaren gidajen cin abinci, da yawon bude ido, da wasannin motsa jiki da kuma harkokin nishadi.
Daga irin kamshin dake tashi a gidajen cin abinci na birnin Zhengzhou zuwa sowar masu sha’awar kwallon kwando a Zhejiang, za a fahimci irin yadda mahukuntan biranen suke bullo da shirye-shiryen bayar da tallafin kashe kudi domin kara kuzarin ruhin walwalar al’umma.
A Guangzhou, ana bai wa masu sha’awar zuwa gidajen cin abinci wata kyakkyawar dama bisa yadda ake raba musu takardun tallafin cin abinci. A karkashin wannan tsari a zagaye na biyar, daga watan Disambar bara zuwa yanzu an raba takardun tallafin adadin yuan miliyan 100 wadda mutane suka yi amfani da su wajen ciye-ciye da tande-tande. Mahukuntan lardin Zhejiang sun fahimci yadda haduwar mutane a wuraren cin abinci ke inganta walwalarsu da kuma kara dankon soyayya da zumunci a tsakaninsu, kana da samar da karin karfi ga tattalin arziki.
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a.
Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya ware makudan kudi yuan miliyan 500 domin karfafa zuwan jama’a wurare da dandaloli na wasannin kwaiwakyo, da wasannin ban dariya, da harkokin wasanni na zamani da sauransu, inda a zagayen farko aka fara kashe yuan miliyan 30. A karkashin wannan tsarin na tallafi, mutane sun kashe fiye da yuan miliyan 91 a bangaren wasanni a birnin na Shanghai.
Shi kuwa lardin Zhejiang ya zo da wani salo ne na musamman mai hangen nesa, inda ya hade wasanni da yawon bude ido a bangaren karfafa walwalar jama’a da kashe kudi. Masu sha’awar kwallon kwando suna amfani da tikitin wasanni mai rangwame da lardin yake bayarwa don garzayawa wuraren wasanni masu jan hankali, da gidajen abinci da sauransu. Yin hakan wata fasaha ce ta karfafa hanyoyin taimakawa ci gaban tattalin arzikin cikin gida ta fuskar tsarin gudanar da rayuwar jama’a.
A can birnin Guangzhou ma, sama da mazauna birnin miliyan 6 ne suka yi amfani da takardun tallafin cin abinci, inda aka kashe yuan miliyan 409. Hakika wannan yana nuna cewa, duk lokacin da aka buda wa mutane sararin shiga a dama da su, to za su yi hakan da zuciya daya kuma cikin jin dadi.
A kwanan nan, wasu mahukunta a kasar Sin sun jaddada bukatar kara fadada hanyoyin cin gajiyar harkokin rayuwa na yau da kullum da ake kashe kudi wajen gudanar da su, don haka wadannan dabaru da gwamnatocin biranen suka bullo da su, suna ba su damar jifan tsuntsu biyu da dutse daya, ga amfanin da za a samu ta fuskar karuwar tattalin arziki musamman ga kananan masu sana’o’i, ga kuma inganta jin dadi da walwalar jama’a. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jaddada bukatar habaka kasuwancin bangaren hidimomi a mataki mai babban inganci, domin bayar da goyon baya mai karfi ga gina kasar Sin a kan turbar zama kasar da ke kan gaba ta fuskar kasuwanci, da kafa sabon tsarin tattalin arziki na bude kofa mai matukar inganci.
Li ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar wani taron nazari da majalisar gudanarwar kasar ta gudanar.
Li ya ce, yayin da yanayin kasa da kasa ke sauyawa, da kuma yadda ake zurfafa sake fasalin masana’antu a cikin gida, dole ne a ba da fifiko kan kirkire-kirkire a cikin harkokin kasuwanci na hidimomi.
Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasar Sin ta himmatu wajen shigo da ayyukan hidimomi masu matukar inganci, da yin amfani da ingantaccen tsarin bude kofa ga waje don inganta masana’antun gudanar da hidimomi na cikin gida, da hanzarta bude kofar hukumomi a fannin hada-hadar gudanar da hidimomi.
Li ya ce, za a yi kokarin samar da kyakkyawan yanayi na shigo da ayyukan hidimomi, da kyautata tsarin kula da manyan iyakokin kasa, da karfafa yadda ake kula da bayanai na iyakokin kasar cikin tsari. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Musiba da auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu.
Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti.
Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahi, lokacin da iyalin ke barci.
Sai dai ya ce “a gaskiya wannan tsohon gini ne da aka bari babu gyara, wanda hakan ne ya sa ya rushe.
“Ba zato ba tsammani kawai ginin ya faɗa musu,” in ji shi.
Tuni dai an yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce, ta cika hannu da wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi da wasu mutum biyar da ta ke zargi da harƙallar saka miyagun ƙwayoyi a jakunkunan matafiya a filin jirgin saman Aminu Kano.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi ya fitar.
Sanarwar ta ce, wani mai suna Mohammed Ali Abubakar mai shekara 55 da aka fi sani da Bello Karama da wasu mutum biyar ne suke harƙallar a filin jirgin, inda suke haɗa hannu da wasu ma’aikata wajen harƙallar.
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.
Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.
“’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar 6 ga watan Agustan bana zuwa Jeddah, sai aka qara wasu jakunkuna da sunan su da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi.”
Ya ce, bayan mutanen sun je karvar jakunkunan su ne sai aka tsare su bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar.
“Binciken mu ya gano Ali Abubakar Mohammed wanda ake kira da Bello Karama ne ya kai jakunkunan a ranar 6 ga watan, wadda ita ce ranar da waɗanda ake zargin suka yi tafiya’.
”Amma sai shi (Ali Abubakar Mohammed) ya hau jirgin Egypt Air zuwa Saudiya, amma ya saka jakunkunan a jirgin Ethiopian tare da waɗanda suka hau.”
Femi ya ce wasu ma’aikatan kamfanin Skyway Aviation Handling Company ne suka shigar da jakunkunan da ke ɗauke da ƙwayoyin, sannan suka rubuta sunan waɗanda aka zarga ba tare da sanin su ba, wanda hakan ya sa hukumomi a Saudiyya suka tsare mutanen.
“Amma bayan bincike, mun tabbatar da cewa waɗanda ake zargi ba su da laifin komai, kawai gungun wau mutane ne suka shirya harƙallar a filin jirgin Aminu Kano.”
Hukumar ta ce, tuni mutum shida sun shiga hannu, sannan akwai huɗu da an riga an gabatar da su a kotu.
Waɗanda ya ce an gabatar a kotu su ne: Ali Abubakar Mohammed (Bello Karama) da Abdulbasit Adamu da Murtala Akande Olalekan da Celestina Emmanuel Yayock.
“Sun tabbatar da hannunsu a aukuwar lamarin, inda Ali ya tabbatar da zuwa jakunkunan. Celestina ta ce ita ta shigar da jakunkuna biyu a kan Naira 100,000, wani mai suna Jazuli Kabir ya ce shi ya shigar da jakunkuna biyu a kan Naira 100,000.”
Ya ce hukumar na aiki da hukumomin Saudiyya wajen wanke waɗanda ake zargi, “Shugaban mu zai tafi Saudiyya domin gabatar da sakamakon binciken da muka yi domin ganin an saki, tare da wanke Maryam Hussain Abdullahi da sauran mutanen guda biyu.”
Hukumar ta nanata cewa a shirye take ta ci gaba da yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar, inda ya ƙara da cewa “babu sani ba sabo” a aikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar Sin ce.
Mai riƙon muƙamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Solomon Atang Hallet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi, kuma ana ci gaba da bincike tsakanin rundunar soji da ta ’yan sanda.
Shaidun gani da ido sun ce, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan sallar Magrib, lokacin da sojoji suka dakatar da wata mota da ke ɗauke da ma’adinai daga wurin haƙar Yalo.
Sai dai direban motar ya biris da dakatarwa ya ƙi tsayawa a shingen da sojojin suka kafa, lamarin da ya sa aka biyo shi har cikin garin Futuk.
A nan ne aka samu hatsaniya tsakanin sojojin da ɗan sandan da ake zargin shi ne yake rakiya motar.
Bayanai sun ce a lokacin da cacar baki ta ɓarke, sai ɗan sandan ya ɗauki bindiga ya harbi shugaban tawagar sojojin a baya, inda aka yi nasarar cafke shi tare da karɓe bindigar, yayin da direban motar ya tsere.
Wata majiya ta tabbatar da cewa motar na ɗauke da ma’adinai masu daraja da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba, tare da zargin cewa ɗan sandan na rakiya ne a wajen aikin.
An garzaya da sojan da aka harba zuwa asibiti a Gombe, amma daga baya ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.
Mazauna yankin Futuk sun ce ƙarar bindigar ta firgita jama’a, inda mazauna da ’yan kasuwa suka rufe shaguna suka gudu gida saboda fargabar tashin hankali.
Wani babban jami’i a Alkaleri ya yaba wa sojojin da suka kai zuciya nesa ba tare da sun ɗauki doka a hannunsu ba, sai dai sun tabbatar da kama ɗan sandan da motar.
Duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya cia, domin bai ɗaga kira ko amsa saƙonni ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Wasu mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki zargin shiga jami’an tsaro cikin harkar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, suna mai cewa lamarin na iya zama barazana ga tsaro da zaman lafiya a jihar.
A halin yanzu, kwamishinan ’yan sandan jihar ya ziyarci kwamandan rundunar soji a Bauchi, Birgediya-Janar U.J. Simon, domin kwantar da hankali da tabbatar an gudanar da sahihin bincike.
A yayin taron manema labaru na musamman game da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin mambobi kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta gudanar da yanin yau Laraba 27 ga watan Agusta, jami’in da ke kula da harkokin ciniki ya gabatar da cewa, adadin cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar ta SCO ya kai wani matsayi na koli a tarihi.
Adadin ciniki a tsakanin kasar Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar a shekarar 2024, ya kai dalar Amurka biliyan 512.4, wanda ya karu da kashi 2.7 bisa dari a kan na shekarar 2023. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
A yau Laraba, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labarai, domin gabatar da cikakken bayani kan yadda ake samun ci gaba, a fannin cinikayyar hidimomi ta kasar Sin, da kuma yadda ake shirye-shiryen bikin baje kolin kasa da kasa na kasar Sin na 2025, game da hada-hadar cinikayyar ba da hidimomi ko CIFTIS.
Bayanan da aka gabatar, sun nuna cewa a rabin farko na shekarar bana, jimilar hada-hadar shige da ficen cinikayyar ba da hidimomi ta kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 3.9, adadin da ya karu da kashi 8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara, wanda hakan ya kafa sabon tarihi a daidai wannan lokacin.
Bugu da kari, an bayyana cewa za a gudanar da bikin CIFTIS na shekarar 2025 a birnin Beijing, tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan Satumba dake tafe, kuma an kammala galibin ayyukan shirye-shirye.
Bikin CIFTIS na bana, zai kunshi nune-nune daga kasashe, da hukumomin kasa da kasa sama da 70. Kuma kusan kamfanoni 2,000 ne suka shirya shiga bikin a zahiri. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe