Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu

[ad_1]



Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Shaibu ya yaba, ya bayyana cewa buɗe cibiyoyin horas da sabbin kuratan sojoji (Depot) a jihohin Kudu zai ƙara ƙarfin rundunar wajen karɓar sabbin ma’aikata a faɗin ƙasa.

Laftanar-Janar Shaibu ya bayyana cewa za a buɗe sabbin cibiyoyin horas da sabbin kuratan sojojin ne a Osogbo da ke Jihar Osun da kuma Abakaliki a Jihar Ebonyi.

Ya bayyana haka ne a yayin bikin yaye sabbin dakarun soji 3,439 da aka yi a Cibiyar Horas da Sabbin Kuratan sojoji (Depot) da ke Zariya, inda ya shawarce su  da su zama masu kishin ƙasa da jajircewa.

Ya yaba wa sabbin sojojin bisa jajircewa, juriya da ƙwarewa da suka nuna a tsawon watannin da suka shafe suna karɓar horo a cibiyar.

Laftanar-Janar Shaibu ya bayyana ranar a matsayin ranar nuni da babban ci gaba wajen cika manufar rundunar sojojin Najeriya ta faɗaɗa karfin ma’aikata.

Ya taya sabbin sojojin murnar kammala horon farko na soja, wanda, a cewarsa, shi ne matakin farko na doguwar tafiyar sadaukarwa, kishin ƙasa, da hidima ga al’umma.

“Kuna shiga rundunar soja ne a wani lokaci mai muhimmanci a tarihin ƙasarmu, lokacin da ƙalubalen tsaro ya yi yawa. Ku ɗauki wannan dama da muhimmanci domin ku zama wani ɓangare na mafita ga matsalolin ta’addanci da rashin tsaro,” in ji shi.

Ya buƙace su da su riƙe gaskiya, ladabi, da bin ƙa’ida a duk inda suka samu kansu, yana mai cewa horon da suka samu (a Depot NA) ya shirya su wajen fuskantar manyan ayyukan soja na zamani.

Janar Shaibu ya bayyana cewa manufar sauya tsarin rundunar soja a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Sojoji na nufin kafa runduna mai ƙwarewa, ɗorewa, da shirye-shiryen fuskantar ƙalubale cikin haɗin kai da sauran hukumomin tsaro.

Ya kuma jinjina wa Kwamandan Depot na Zariya, Janar Ahmadu Bello Muhammad, da malamai da jami’an horo saboda jajircewarsu wajen ganin an kammala horon cikin nasara.

Haka kuma, Babban Hafsan Sojoji ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, wanda shi ne Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa rundunar, tare da godewa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da al’ummar Zariya saboda kyakkyawar alaƙa da rundunar soja.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *