Babandede Ya Sabunta Rajistarsa Ta Jam’iyyar APC A Mazaɓarsa Ta Hadejia A Jihar Jigawa

[ad_1]

Tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Muhammad Babandede, a ranar Lahadi 16, ga Febarairun 2026 ya sabunta rajistar zamansa ɗan jam’iyyar APC a Hadejia, Jihar Jigawa.

Babandede ya samu gagarumar tarba daga dimbin magoya baya da suka tarbe shi daga ƙofar gari har zuwa mazabarsa ta Kasuwar Ƙuda. Tafiyar mintuna kaɗan ce, amma ta ɗauki sama da awa huɗu saboda yawan jama’ar da suka fito.

  • APC Ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa
  • Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa

Muhammad Babandede ya yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Ɗanmodi, tare da tabbatar da goyon bayansa ga su da jam’iyyar APC.

Dattijo kuma gogaggen ɗan siyasa Ambasada Haruna Ginsau da Shugabannin jam’iyyar APC sun yaba masa kan biyayya da sadaukarwarsa ga jam’iyya.

Abin da aka tsara ya ɗauki ‘yan mintuna Amma ya ɗauki sama da awa huɗu saboda yawan jama’a daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa, musamman mazaɓar sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *