Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
[ad_1]
Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce ba zai taɓa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba, duk da yadda wasu gwamnoni ke barin PDP suna komawa APC.
Abaribe ya faɗi hakan ne yayin wata hira a gidan talabijin na Channels.
Ya ce shi ne mutum na ƙarshe da zai taɓa shiga APC, yana tambayar dalilin da ya sa gwamnoni da suka yi adawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 yanzu suke shiga jam’iyyarsa.
Sanatan ya kuma ce ‘yan Nijeriya na fama da tsananin wahala saboda taɓarɓarewar tattalin arziƙi da matsalar tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, wannan daliai zau sa Tinubu ba zai yi nasara a zaɓen 2027 ba.
Ya ƙara da cewa yanzu ‘yan ƙasa sun waye kuma a shirye suke su kare ƙuri’unsu, yana mai cewa zaɓen gaba ba zai ƙare da sanarwa cikin dare ba.
[ad_2]
Source link