APC Za Ta Karɓi Gwamnan Filato A Watan Janairun 2026
[ad_1]
Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa za ta karɓi Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, zuwa jam’iyyar a hukumance a watan Janairun 2026.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne, ya bayyana hakan, inda ya ce sauyin jam’iyyar gwamnan zai ƙarfafa APC.
- Sarki Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe kwana 25 A Hannun Masu Garkuwa A Kwara
- Gwamnati Na Tuhumar Malami Da Ɗansa Kan Laifuka 16 Na Almundahanar Kuɗaɗe
Ya yi alkawarin shirya taro mai kayatarwa kuma ya nuna amincewarsa da samun nasarori a zaben gaba.
Tsohon Gwamna Simon Lalong ya yaba wa mambobin jam’iyyar bisa biyayya da haɗin kai, ya kuma yi kira da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya.
Shugaban APC na jihar, Rufus Bature, da Shugaban Majalisar Mashawarta, Danladi Wuyep, sun nuna goyon bayansu, inda suka yaba da yawan halartar mambobin jam’iyyar a taron.
Yilwatda ya kara da cewa APC na maraba da dukkanin ‘yan Nijeriya masu tasiri da suke son shiga jam’iyyar, inda ya jaddada cewa jam’iyyar na son haɗin kai a kowa jihar.
Jam’iyyar ta kuma yi wa mambobinta alkawarin cewa sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan ba za su shafi haɗin kan jam’iyyar ko shirinta ba, tare da bukatarsu da su ci gaba da goyon bayan shirye-shirye da manufofin jam’iyyar a shirye-shiryen zabe mai zuwa.
[ad_2]
Source link