Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai
[ad_1]
Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun.
An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a daidai wurin musayar hanyar.
Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara.
Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima da kuma rashin kula daga ɓangaren direban.
Akinbiyi ya ce, har yanzu ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba, amma ana ci gaba da aikin ceto kan gobarar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Al’amarin tashin gobara da wata tankar mai ɗauke da man fetur lita 30,000 ta faɗi man cikinta kuma ya zube da tsakar daren yau da misalin ƙarfe 0100 (1 na tsakar dare), a kan hanyar Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagam a musayar hanya ta babban titin PMB, sakamakon gudun wuce gona da iri da aka samu.
“Sakamakon abin takaicin ya kuma shafi ƙona wata babbar mota da wata mota a gefen hanya, da kuma lalata wata wayar wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga Mowe da kewaye.
“Duk da cewa ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu a halin yanzu ba, jami’an agajin gaggawa na hukumar kashe gobara ta TRACE, a jihar Ogun da Nestle PLC, da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa FRSC da ‘yan sanda suna nan a ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan kashe gobarar da tada hankula.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link