An zargi Gwamnan Bauchi da biyan $9.7m don ɗaukar nauyin ta’addanci
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta danganta Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da ya kai kimanin dala miliyan 9.7.
A ranar Laraba, Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta gurfanar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, tare da wasu mutum uku a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ana zarginsu da haɗa baki wajen karkatar da kuɗin gwamnati da kuma amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin ta’addanci.
Sauran waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed.
Ana tuhumar su ne bisa dokokin hana safarar kuɗi da ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya.
Mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Janairu, 2026.
Dukkanin waɗanda ake tuhuma sun musanta laifin da ake zarginsu da shi.
Lauyan EFCC ya buƙaci kotu ta fara shari’ar domin gabatar da shaidu da hujjoji.
Lauyan da ke waɗanda ake tuhuma, Gordy Uche (SAN), ya nemi kotu ta bayar da belinsu.
Ya ce tsare Kwamishinan Kuɗi ya janyo tsaiko wajen biyan albashin ma’aikatan Jihar Bauchi sama da mutum 60,000.
Sai dai EFCC ta ƙalubalanci buƙatar bayar da belin nasu.
EFCC ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2024, Yakubu Adamu da sauran waɗanda ake tuhuma sun bai wa Bello Bodejo da abokan hulɗarsa kuɗi dala miliyan 2.3, bisa umarnin Gwamna Bala Mohammed.
Hukumar ta kuma ce an ƙara bayar da dala miliyan 7.4 ta hannun wani ɗan canjin kuɗi.
EFCC ta ce ya kamata waɗanda ake tuhuma su san cewa za a iya amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin ta’addanci.
Wani sashe na tuhumar ya ce an bayar da kuɗin ne da sanin cewa za a iya amfani da su wajen tallafa wa ’yan ta’adda, wanda hakan ya saɓa wa dokokin Najeriya.
Martanin Gwamna Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa kan yadda ake ƙoƙarin danganta shi da ta’addanci.
Ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin karɓar lambar yabo ta Jakadan Tsaro daga Cibiyar Tsaro ta Najeriya (ISPON).
Ya ce abun mamaki ne yadda aka ambaci sunansa a kotu duk da yana da kariya a kundin tsarin mulki a matsayinsa na gwamna mai ci.
Gwamnan ya ce tsare Kwamishinan Kuɗinsa da EFCC ke yi babban zalunci ne ga gwamnatinsa.
Ya zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da EFCC da kotuna wajen gallazawa da tsoratar da ’yan adawa.
Ya ce ana amfani da hukumomin gwamnati wajen cin zarafin waɗanda ba sa cikin jam’iyya mai mulki.
Gwamna Bala Mohammed ya yi gargaɗin cewa idan ba a daina yin hakan ba, zai iya janyo rikicin siyasa.
Ya kuma soki Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa duk da yawan kuɗaɗen shiga da ta ke samu, ba a ga gagarumin ci gaba a Bauchi ba, musamman a ɓangaren tituna, gine-gine da ayyukan more rayuwa.
Ya ce ya daɗe da kame bakinsa domin zaman lafiya, amma ba zai ci gaba da amincewa da tsoratarwa da danniya ba.
Ya jaddada cewa ba za a tilasta masa barin jam’iyyar PDP don komawa APC ba.
Gwamnan ya ƙara da cewa an kama wasu ’yan uwansa da jami’an gwamnatinsa ba tare da wata hujja ba, inda ya ce aikata hakan bai dace da dimokuraɗiyya ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link