An kama ɓarayi da motocin da aka sace a Gombe
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu nasarar gano wasu motoci da aka sace tare da kama wasu da ake zargin ɓarayi ne masu aikata laifuka ciki har da ƙwace bindiga ƙirar gida.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bello Yahaya, inda ya ce nasarorin sun biyo bayan sintiri da sahihan bayanan leƙen asiri da haɗin gwiwar al’umma.
A cewar sanarwar, a ranar 13 ga Oktoba, 2025, jami’an sashin Balanga sun gano wata mota ƙirar Toyota Jeep launin baƙi da lambar rijista ABUJA, ABC 241 DW a hanyar Bangu–Laura a Ƙaramar hukumar Balanga
Barayin motar sun yi ƙoƙarin tsere wa bayan ganin ’yan sanda, inda suka kai wa jami’ai hari da ƙaramar bindiga ƙirar gida kafin su bar motar suka gudu da babur.
Bincike ya gano takardun motoci biyu ƙirar Lexus, kuma daga baya aka tabbatar cewa motar asali Lexus Jeep ce mai launin toka da aka sake launinta kamar Toyota Prado, wadda aka sace daga Abuja a ranar 5 ga Oktoba.
Rundunar ta ce, tana aiki da rundunar Abuja don kamo waɗanda suka tsere.
Haka kuma, a ranar 15 ga Oktoba, 2025, ’yan sanda daga sashin Gombe sun kama Sani Bappari, mai shekara 45 daga unguwar Mallam Inna, bisa zargin satar mota ƙirar Honda Civic da lambar rijista DKU 564 AA, wadda aka sace a tsakiyar gari
An same ta a hannunsa kuma yanzu haka tana hannun ’yan sanda a matsayin shaida.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link