Amurka ta gabatar da matakai 15 domin kawo ƙarshen yaƙinta da Iran

[ad_1]



Gwamnatin Amurka ta gabatar da wani sabon tsari mai ƙunshe da matakai 15 da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi da ƙasar Iran.

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Pakistan ce ta taka rawar gani wajen isar da wannan ƙudiri ga mahukuntan Tehran a matsayinta na mai shiga tsakani.

Babban maƙasudin shirin shi ne tabbatar da cewa Iran ta janye aniyarta na ƙera makaman nukiliya.

Daga cikin sharuɗan da ke ƙunshe a ciki akwai cewar Iran ta amince ba za ta ƙera makaman nukiliya ba.

Miƙa dukkanin uranium da ta riga ta inganta ga Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Wakili na musamman na Amurka, Steve Witkoff, ya bayyana cewa Iran ta riga ta nuna alamun amincewa da wasu muhimman sassan shirin, musamman batun miƙa uranium.

Shi kansa Shugaba Donald Trump ya jaddada cewa akwai alamun Iran na son cimma matsaya ta bai-ɗaya.

Duk da wannan ci gaban da aka samu, har yanzu gwamnatin Iran ba ta fito ta bayyana matsayarta a hukumance ba.

Haka kuma, ba a bayyana matsayar ƙasar Isra’ila ba game da wannan sabon shiri.

Manyan jami’an gwamnatin Amurka, ciki har da Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio da Mataimakin Shugaban Ƙasa, JD Vance, na sahun gaba wajen gudanar da wannan tattaunawa domin ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *