ADC ta yi watsi da sabon jadawalin Zaɓen 2027 da INEC ta fitar
[ad_1]
Jam’iyyar ADC ta yi watsi da sabon jadawalin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar domin zaɓukan 2027
Jam’iyyar ta ce jadawalin ya ƙunshi wasu sharuɗa da za su iya hana jam’iyyun adawa shiga zaɓe yadda ya kamata.
Jami’yyar ta kuma ta yi zargin cewa canje-canjen na iya bai wa Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaɓen 2027.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce yanzu ana buƙatar jam’iyyu su miƙa sunan mambobin da aka yi wa rajista ta Intanet kafin fara zaɓen fidda gwani a ƙarshen watan Afrilu.
Jam’iyyar ta ce wannan wa’adi ya yi kaɗan kuma zai iya hana wasu jam’iyyu gabatar da ’yan takara.
Ta kuma yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta fara shirin rajistar ’ya’yanta da wuri, domin samun dama sama da kowace jam’iyya.
ADC ta ce tana haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun adawa domin ƙalubalantar jadawalin, tare da kira ga ’yan Najeriya da ƙungiyoyi da su duba batun domin tabbatar da adalci yayin gudanar da zaɓe.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link