Abin da ya sa na sauka daga muƙamin Mataimakin Gwamnan Kano — Gwarzo
[ad_1]
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana cewa murabus ɗinsa ba shi da alaƙa da matsin lamba da yake fuskanta, illa dai don tabbatar da zaman lafiya, daidaito da kuma ci-gaba mai inganci a jihar.
A cikin wasiƙar da ya aika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ranar 27 ga Maris, 2026, Gwarzo ya ce murabus ɗin nasa na son rai ne, kuma ya yi shi da kyakkyawar niyya.
“Na ɗauki wannan mataki ne a cikin ruhin alhakin shugabanci, domin ba da damar gwamnati da jihar su ci gaba ba tare da wata tangarɗa ba,” in ji shi.
Ya ce matakin ya biyo bayan shawarwari da tunani mai zurfi kan halin siyasar jihar.
Gwarzo ya jaddada cewa murabus ɗin ba ya nufin amincewa da aikata wani laifi, sai dai ƙoƙarinsa na kare mutuncin gwamnati da kuma tabbatar da darajar dimokuraɗiyya.
“Wannan murabus na son rai ne, kuma bai kamata a ɗauke shi a matsayin amincewa da wani laifi ba, illa dai mataki na hidimar jama’a,” in ji shi.
Gwarzo ya jingina murabus ɗin nasa da Sashe na 306(2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya ba wa masu riƙe da muƙaman gwamnati damar sauka daga kujerunsu.
Ya gode wa al’ummar Kano bisa damar da suka ba shi na yi musu hidima, tare da gode wa gwamna, mambobin majalisar zartarwa, majalisar dokoki ta jihar, Jam’iyyar NNPP, masarautu da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake riƙe da muƙamin.
Murabus ɗin Gwarzo ya zo ne a daidai lokacin da ake cikin rikice-rikicen siyasa da shari’a kan ofishin mataimakin gwamna a Kano, inda majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link