Bukayo Saka ya zama ɗan wasa mai albashi mafi tsoka a Arsenal

[ad_1]



Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Bukayo Saka, ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar kaka biyar da za ta ci gaba da riƙe shi a kulob ɗin har zuwa shekarar 2031.

Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa sabon kwantiragin ya mayar da Saka ɗan wasa mafi karɓar albashi a Arsenal, inda ake sa ran zai riƙa samun sama da fam 300,000 duk mako.

Rahotanni sun ce an shafe kusan shekara guda ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu kafin a kai ga cimma matsaya.

Tun a watan Janairu ne Saka ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da zama a Gunners, duk da cewa tsohon kwantiraginsa — wanda ya sabunta a 2023 — zai ƙare ne a 2027.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Arsenal ke fafatawa a gasanni daban-daban, inda take jagorantar teburin gasar Premier League da tazarar maki huɗu a gaban Manchester City.

Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama na kuma shirin karawa da Manchester City a wasan ƙarshe na Carabao Cup a watan Maris.

Bugu da ƙari, Gunners ta kai zagaye na biyar a FA Cup karon farko cikin kaka shida, sannan ta tsallake zuwa zagaye na gaba a UEFA Champions League bayan kammala wasannin rukuni tana mataki na ɗaya.

A bana, Saka ya zura ƙwallo bakwai a wasanni 33 da ya buga, lamarin da ya ƙara tabbatar da muhimmancinsa a cikin tsarin Arteta.

Sabuwar yarjejeniyar na daga cikin shirin Arsenal na riƙe manyan ’yan wasanta domin ƙarfafa yunƙurin komawa lashe manyan kofuna, ganin cewa rabonta da babban kofi tun 2020.

Arsenal ta kai zagaye na biyar a FA Cup karon farko a kaka shida

Arsenal ta zura ƙwallo 4-0 a minti na 30 da take leda da ta kai ta doke Wigan a FA Cup ta kuma kai zagaye na biyar a karon farko a kaka shida.

Wadda take ta ɗaya a kan teburin Premier League ita ce ta mamaye wasan da ta yi da mai buga League One da fara cin kwallo tun a minti na 11 da fara karawar.

Rabon da Arsenal ta kai zagaye na biyar a kofin tun 2020 – lokacin da Mikel Arteta ya karbi aikin jan ragamar Gunners da daukar FA Cup.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *