Ɗan sanda ya mayar da miliyan 2.6 da aka yi kuskuren tura masa
[ad_1]
Wani jami’in ɗan sanda mai mukamin kurtu a Jihar Borno, Muhammad Alhaji Muhammad, ya mayar da kuɗi har Naira Miliyan 2.6 da aka yi kuskuren tura masa zuwa asusun ajiyarsa na banki.
Ya ce matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga burinsa na kare martabar Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya.
Rahotanni sun ce Muhammad, wanda ke aiki a Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno, ya samu kuɗin ne ba zato ba tsammani daga wani amfani da bankin hada-hadar kuɗi na Moniepoint.
Sai dai nan da nan ya ɗauki matakin tabbatar da cewa kuɗin sun koma hannun mai su.
Wannan abin da ya aikata ya jawo yabo daga jama’a, inda wani mai amfani da shafukan sada zumunta, mai suna Bello Jafar, ya bayyana farin cikinsa da yadda jami’in ya nuna gaskiya da amana yayin hidimar ƙasa.
A cikin wani rubutu da aka yada a intanet, Jafar ya bayyana Muhammad a matsayin “Jami’in ɗan sanda mai gaskiya,” yana mai cewa halayensa sun nuna kyawawan dabi’u da ake tsammani daga ma’aikatan gwamnati.
Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Naziru Abdulmajeed, ya gayyaci jami’in zuwa wani taro bayan yabon da jama’a suka yi masa kan matakin da ya ɗauka.
ASP Daso ya ce Muhammad, wanda ke aiki a sashen inshora na rundunar, ya samu sanarwar shigar kuɗin a ranar Alhamis.
Amma nan da nan ya fahimci cewa kuskure aka yi, kasancewar ba a yi masa tanadin kuɗin daga ko’ina ba, don haka ya hanzarta mayar da su ga mai su.
An bayyana wannan matakin a matsayin kyakkyawan misali na gaskiya a cikin rundunar, da kuma tunatarwa cewa irin waɗannan ayyuka na gaskiya na iya ƙarfafa amincewar jama’a ga jami’an tsaro.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link