Fasinjoji 4 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a hanyar Abuja-Lokoja

[ad_1]



Aƙalla fasinjoji huɗu ne suka rasu sakamakon wuta da ta kama wata mota ƙirar bas mai kujeru 18, da ta yi hatsari a kan titin Abuja zuwa Lokoja kusa da ƙauyen Yangoji.

Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Asabar da misalin ƙarfe 7:59 na safe.

Motar, mai lambar AKK 288 ZA, ta fito ne daga yankin Lokoja lokacin da ta ƙwace qa direban.

Wani ganau ya ce motar tana gudun wuce ƙima ne lokacin da ta sauka daga kan hanya, ta faɗa cikin rami sannan ta kama da wuta.

Adadin fasinjoji 22 maza ne a cikin motar.

Huɗu daga cikinsu sun rasu sakamakon tashin wutar, yayin da sauran 18 suka samu raunuka.

Daga baya jami’an ceto sun kwashe gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa na asibiti.

Wani jami’in Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) da ya halarci wajen ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce waɗanda suka jikkata sun samu raunin ƙuna, karaya da sauran sauransu, kuma an kai su asibitoci daban-daban ciki har da Asibitin Rhema da ke Kwali domin kula da lafiyarsu.

Jami’an FRSC tare da ’yan sanda na sashen Kwali ne suka gudanar da aikin ceton tare.

Mahukunta sun danganta hatsarin da gudun wuce ƙima, wanda hakan ya yi sanadin aukuwar hatsarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *