Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban NAHCON
Shugaba Bola Tinubu ya nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta Nijeriya (NAHCON).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa kan harkokin yada Labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba.
“Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙa a yau, yana neman a tabbatar da Ambasada Yusuf cikin gaggawa don maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan makon, bayan kimanin watanni 14 a kan mukamin,” in ji sanarwar.
Nadin, wanda aka sanar a ranar Laraba, dole yana buƙatar amincewar Majalisar Dattawa bisa ga tanadin Sashe na 3(2) na Dokar NAHCON.