Bikin Bazara Na Sinawa Na Zama Tambarin Al’adu Na Duniya
Bikin bazara shi ne bikin gargajiya mafi girma a kasar Sin. Bisa shigar da “bikin bazara da ya kasance bikin al’adar zamantakewar Sinawa na murnar sabuwar shekara ta gargajiya” a cikin jerin harkokin al’adun gargajiya na UNESCO, yadda duniya ke kara amincewa da wannan alama ta al’ada ya karu sosai.
Bikin bazara yana dauke da walwala mai motsa zuciyar dan’adam a duniya. A lokacin bikin bazara, mutane suna murnar sake haduwar iyali, kuma yayin da suke bankwana da tsohuwar shekara, da yin maraba da sabuwar, su kan cika da bege da kyakkyawan fata na rayuwar gaba. Wannan walwala mai motsa zuciya ita ce ainihin abin da ake nema a cikin zukatan mutane daga dukkan al’ummomin kasashen duniya.
Karuwar ‘yan kasashen waje da ke murnar sabuwar shekarar Sinawa, da kuma tashen da yanayin bikin bazara ke samu, sannu a hankali suna zama wani sabon yanayi da ke tashe a duniya. Yana kuma nuna cewa, tunanin Sinawa da ake wa “kallo daga nesa” yana canzawa zuwa “kallo na kusa”. Sannan galibin mutane daga kasashe daban-daban, ba wai kawai suna lura da kasar Sin daga nesa ba ne, amma suna kara kusanto kasar ne a aikace, da gano yadda take da kuma fahimtar ta. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)