’Yan bindiga sun sace matafiya 16 a Benuwe

[ad_1]



Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla matafiya 16 a kan babbar hanyar Utonkon–Okpoga da ke Jihar Benuwe.

Lamarin na zuwa ne bayan ’yan bindigar sun kai hari kan wata motar haya da ke ɗauke da fasinjoji daga Ƙananan Hukumomin Oju da Obi zuwa yankunan yammacin ƙasar.

Wannan sabon harin ya auku ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan sace mutane tara daga wani coci da ke garin Utonkon a Ƙaramar Hukumar Ado ta jihar.

Waɗanda suka shaida sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar Litinin, a kan hanyar da ta haɗa Ƙananan Hukumomin Ado da Okpokwu.

Wani jagoran matasa a unguwar Utonkon, Kwamared Jude Onwe, ya shaida cewa motar na ɗauke da matafiya 16 ’yan ƙabilar Igede, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Okpoga a Ƙaramar Hukumar Okpokwu lokacin da ’yan bindigar suka tare su.

Onwe ya ce fasinjojin sun taso ne daga kasuwar Iheijwo da ke Ƙaramar Hukumar Oju, suna kan hanyarsu zuwa wurare daban-daban a yammacin ƙasar, kafin a tare su bayan sun tsallaka yankin Utonkon–Ojapo/Okpoga a Ƙaramar Hukumar Ado.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Oju, Jackson Ominyi, ya ce lamarin ya rutsa da gaba ɗaya fasinjoji 16, inda aka kashe mutum biyu, yayin da aka ceto wasu biyu.

Ominyi ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen biyun ta hanyar haɗin gwiwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Okpokwu, yana mai ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da neman sauran matafiya 12 da aka sace.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe, DSP Udeme Edet, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aike masa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *