Ɗalibi ya Rasu Kan Zargin Yi Masa Dukan Tsiya A Yobe
[ad_1]
Wani ɗalibi da ke aji na ƙarshe (SS3) a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnati (GSTC) da ke Potiskum a Jihar Yobe, ya riga mu gidan gaskiya.
Ana zargin ya rasu ne sakamakon cin zarafi da wasu abokan karatunsa suka yi masa.
- NiMet Ta Yi Hasashen Ƙwallewar Rana Da Gajimare Na Kwana Uku, Litinin – Talata
- Ka Manta Da Komai, Ka Bar Abba Ya Yi Wa Kano Aiki — Matar Ganduje Ga Kwankwaso
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, inda ake zargin wasu ɗalibai da kai wa mamacin hari.
Sai dai har yanzu ba a tantance takamaiman dalilin da ya yi sanadiyyar ajalinsa ba.
Tuni dai aka binne ɗalibin a garinsu na Gadaka, da ke Ƙaramar Hukumar Fika a jihar.
Kakakin Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa tuni rundunar ta ƙaddamar da bincike don kamo bakin zaren.
“E, muna da masaniya kan faruwar wannan al’amari, kuma bincike na gudana domin gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in ji shi.
Hakazalika, wani malami a makarantar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mahukuntan makarantar sun miƙa ɗaliban da ake zargi da hannu ga hukuma domin zurfafa bincike.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Yobe, Farfesa Abba Idriss Adam, ya bayyana cewa zai yi cikakken bayani kan lamarin nan gaba bayan ya tattara bayanai.
[ad_2]
Source link