An kashe ɗan bindiga da kama wasu a Benuwe
Dakarun rundunar Sojojin haɗin gwiwa ta Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wani ɗan bindiga tare da kama wasu mutane takwas da ake zargi da aikata laifuka a cikin haɗin gwiwar ayyukan tsaro a jihohin Benuwe da Nasarawa.
A cikin wata sanarwa da kakakin OPWS, Laftanal Ahmad Zubairu ya fitar, ya ce dakarun sashe na 1, OPWS, a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2026, da ke aiki da sahihan bayanan sirri game da tafiye-tafiyen makiyayan da ke ƙauyen Ayamba da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala a Jihar Benuwe, sun ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa tare da jami’an ’yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farar hula na jihar Benuwe.
Zubairu ya bayyana cewa, sojojin sun yi artabu da ’yan bindigar ne da isar su, wanda hakan ya haifar musayar wuta inda aka kashe ɗan bindiga guda ɗaya.
Ya ce, an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsashi mai girman 7.62mm × 39 da kuma kunson harsashi guda biyu a wurin.
Kakakin ya ƙara da cewa, a wani samame mai alaƙa da shi a ranar 4 ga Fabrairu, 2026, dakarun sashe na 2, OPWS, da aka tura sintiri a sansanin Base Agyaragu a jihar Nasarawa, sun kama wani da ake zargin ɗan fashi da makami ne a hanyar Asupe – Ome a ƙaramar hukumar Obi, biyo bayan bayanan sirri da wani mafarauci ya bayar.
Ya ce, wanda ake zargin mai suna Adam Paul ɗan shekara 34, an kama shi da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, inda ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa, an samu makamin ne daga wani Tela Obu na unguwar Duduguru a ƙaramar hukumar Obi.
Zubairu ya bayyana cewa, wasu mutane biyun da ake zargin John Amos da Elisha, waɗanda suma ’yan unguwar ɗaya ne, sun gudu daga yankin, kuma a halin yanzu suna hannun su, inda ake ci gaba da tsare su.
Ya ci gaba da cewa, a wannan rana, dakarun COAS Interɓention Battalion IX, da aka tura a Agbaragba a jihar Benuwe, sun amsa kiran da aka yi musu na satar shanu da ake zargin matasan unguwar Agagbe ne suka yi.
Ya ce an gano matattun shanu da dama a wurare daban-daban, yayin da aka kama wasu mutane uku da ake zargin an miƙa su ga rundunar ’yan sandan Najeriya da ke Naka domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.