‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Kan Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Man Fetur A Bauchi


‘Yansanda a jihar Bauchi sun yi nasarar cafke mutum biyu kan zargin safarar man fetur ga ‘yan bindiga, a garin Mansur, da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar.

An kama wadanda ake zargin, Ayuba Ahmadu da Danlami Ayuba, dukkansu ‘yan shekara 25, da man fetur lita 560 a lokacin d suke kokarin kai wa ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a yankin.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a hedikwatar rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, kakakin rundunar, SP Nafi’u Habib, ya ce, kamawar ta biyo bayan ci gaba da ayyukan leken asiri da ake gudanarwa da nufin katse hanyoyin da ‘yan bindigar ke bi wajen samun kayayyakin da suke amfani da shi.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin kowane a kan babur kirar Honda, dauke da lita 280 na man fetur a cikin jarkoki, wanda hakan ya haifar da shakku a gare su nan take.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *