ICPC Ta Kama Tsohon Shugaban NIMASA, Bashir Jamoh
[ad_1]
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (ICPC) ta kama tsohon Darakta-Janar na NIMASA, Bashir Jamoh, kan zargin amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida ba.
Jamoh, wanda ya shugabanci NIMASA daga 2020 zuwa 2023, an tsare shi ne bayan ya ƙi amsa gayyatar ICPC sau da dama dangane da ƙorafe-ƙorafe da aka shigar kansa.
- Rashin Isassun Makarantu Ke Sa Ana Yi Wa Yara Auren Wuri A Arewacin Nijeriya – Sarkin Kano
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, Sun Ƙone Gidaje A Ƙauyukan Kwara
Ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafe na zarginsa da amfani da muƙaminsa wajen cin moriya don amfanin ƙashin kansa ta hanyar almundahana a wasu kwangiloli.
Mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya tabbatar da kama shi amma bai yi cikakken bayani kan zargin ba.
A baya Jamoh ya musanta zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Ya taɓa roƙon EFCC ta binciki zargin da ake masa kan karkatar da maƙudan kuɗaɗen.
[ad_2]
Source link