Wani riƙaƙƙen ɗan daba ya faɗa komar ’yan sanda a Kano

[ad_1]



Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani riƙaƙƙen ɗan daba mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, a unguwar Ɗorayi da ke birnin Kano, bisa zargin jagoranci da shirya ayyukan daba da yi wa jama’a fashi da makami.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an kama Auwalu mai shekaru 26 ne ranar 31 ga watan Janairun 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Kiyawa ya ce jami’an ‘yan sanda reshen unguwar Dorayi ne suka cafke Auwalu wanda ake zargin ya shahara wajen haɗa gungun ‘yan daba domin kai hare-hare da ƙwace dukiyoyin mutane.

Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa jami’anta da ke yankin unguwar Sharada sun amsa kiran gaggawa kan harin da wani da ake zargin ɗan fashi ne ya kai har ya yi wa wata mata lahani, lamarin da ya kai jama’a sun yi masa dukan kawo wuƙa.

Sanarwar ta ce an garzaya da matar da aka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano domin ceto rayuwarta, inda wani jami’in ɗan sanda ya ba da jininsa domin taimakawa wajen ceton rayuwar matar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewa da sadaukarwar jami’an, musamman jami’in da ya ba da jininsa domin ceton rai, tare da gode wa al’ummar Kano bisa ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai da goyon baya.

Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta lambobin gaggawa na rundunar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *