An Fitar Da Sakon Bidiyo Na Yayata Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Afirka Ta Kudu
[ad_1]
A ranar 31 ga watan Janairu ne babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya kammala bitar zagaye na uku ta shirye-shiryen bikin bazara ko bikin shiga sabuwar shekarar Sinawa ta 2026 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.
Yayin da ake gudanar da ayyukan shirya bikin, an nuna sakon bidiyo na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG karo na farko a Johannesburg, birni mafi girma a Afirka ta Kudu, inda aka mika gaisuwar sabuwar shekara daga kasar Sin zuwa ’yan asalin kasar Sin dake zaune a Afirka da Kudu da kuma al’ummar kasar kafin zuwan bikin.
Yayin bikin, an nuna bidiyon yayata shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2026 a babban maijigi, inda hotuna masu kayatarwa da sanya farin ciki na sabuwar shekarar Sinawa suka jawo hankulan baki sosai. Jigon shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2026 shi ne “Ba za a iya tsayar da gudun dawaki ba”, wanda ya yada ruhin zamanin da muke ciki, kuma an isar da shi ne daga kasar Sin zuwa Afirka a karon farko.
Johannesburg, birni ne dake tattare da ’yan asalin kasar Sin mazauna wurin sama da 300,000. Wannan ne karo na farko da aka nuna sakon na yayata shirye-shiryen murnar bikin bazara a wurin, kuma ’yan asalin kasar Sin dake zaune a wurin da yawa sun yi tattaki na musamman zuwa wurin don daukar hotuna a gaban bangon dake dauke da jigon shirye-shiryen murnar bikin bazarar Sinawa, don ajiye abubuwan tunawa game da murnar bikin bazara. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link