Ko APC Ta Fara Zawarcin Jagoran Kwankwasiyya Ne?
[ad_1]
Shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar mai mulki a shirye take ta tarɓi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan sake fasalin siyasa da kuma hasashe a siyasar jihar Kano, wanda hakan ya jawo Kwankwaso mayar da martani.
- Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram, Abu Khalid, Da Wasu 10 A Borno
- Magidanci Ya Kashe Mutumin Da Yake Zargin Hulɗa Da Matarsa A Yobe
In ba a manta ba, gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, kwanan nan ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar da na wakilai.
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV a ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar APC ya ce, duk da cewa jam’iyyar ba ta tattaunawa da Kwankwaso a yanzu, amma za a karɓe shi da kyau idan ya zaɓi sauya sheƙa zuwa APC.
“Ƙofofinmu na APC a buɗe suke ga Kwankwaso. Idan ya zo, zai samu tarba babba. Duk da cewa har yanzu ba mu tattauna da shi ba,” in ji Yilwatda.
[ad_2]
Source link