Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram, Abu Khalid, Da Wasu 10 A Borno
[ad_1]
Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) sun hallaka wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Abu Khalid tare da wasu ƴan ta’adda 10 a dajin Sambisa, Jihar Borno. Lamarin ya faru ne kwana guda bayan da sojojin sashi na 1 tare da ‘yan CJTF suka hallaka Julaibib, wani kwamandan Boko Haram/ISWAP da ke aiki a yankin Gujba na Timbuktu Triangle.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, ya ce an samu nasarar ne a daren Asabar bayan sojoji sun yi artabu da ƴan ta’adda a yankin Komala, Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno, da misalin ƙarfe 11 na dare.
- Sojoji Sun Kama Tsohuwa Mai Shekaru 65 Bisa Zargin Safarar Ƙwayoyi Ga Ƴan Boko Haram
- Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Sojoji A Borno
Uba ya bayyana cewa Abu Khalid ya kasance muhimmin jigo a tsarin Boko Haram, yana da alhakin shirya ayyuka da kula da kayan aiki a yankin Sambisa. Bayan artabun, sojoji sun ƙwato bindigogi AK-47 guda biyar, da sinƙin harsashi, da kekuna, da kayayyakin abinci da na magani masu yawa.
Ya ƙara da cewa babu wani rauni ko asara a ɓangaren sojoji, inda ya jaddada cewa ayyukan kakkaɓe dajin na ci gaba a Sambisa, da dutsen Mandara da Timbuktu Triangle domin murƙushe ragowar ƴan ta’adda Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.
A wani ɓangare guda, sojojin sun hallaka adadi mai yawa na ƴan bindiga a Jihar Zamfara a wani sumame na haɗin gwuiwar ƙasa da sama a sansanin shahararren shugaban ƴan bindiga Gwaska Ɗan Karmi a Ƙaramar Hukumar Maru. An ce rundunar sojin ƙasa, tare da tallafin Rundunar Sojin Sama, ta kai harin ne bayan bayanan sirri sun nuna cewa sama da ƴan bindiga 100 sun taru domin shirya hare-hare kan al’ummomi da hanyoyin isar da kayan soji.
[ad_2]
Source link