2027: Atiku Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabannin Jam’iyyar ADP Kan Jita-Jitar Takarar Obi Da Kwankwaso

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya gudanar da wani taro na sirri da shugabannin Jam’iyyar ADP a gidansa da ke Abuja a karshen mako.

Shugaban Jam’iyyar ADP na ƙasa, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan tattaunawa da manyan shugabannin siyasa domin karfafa dimokiraɗiyya gaban zaɓen 2027, tare da ƙarfafa dimokiraɗiyya da daidaita matsayin jam’iyyun adawa.

  • Atiku Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Gaggauta Gyara Dokar Zabe Don Hana Magudi A 2027
  • Yadda Buƙatun Kwankwaso Suka Tarwatsa Yiwuwar Haɗin Gwuiwa Da APC

A cewar sanarwar da Sani ya fitar, tattaunawar ba ta shafi haɗa jam’iyyu ko karɓar sababbin mambobi cikin ADP ba.

Sai dai, masu sharhi a harkokin siyasa sun lura cewa wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar yiwuwar haɗin guiwa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, domin ƙarfafa adawar da za ta fuskanci jam’iyyar mai mulki a 2027.

Sani ya ƙara da cewa ADP ta mayar da hankali kan tsaftace jam’iyya da tabbatar da zabuka masu inganci ga ‘yan ƙasa, inda duk wata shawara da za ta taso za a yi ta ne kan gaskiya da adalci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *