A.A. Zaura Ya Wakilci Gwamna Abba Wajen Karɓo Lambar Yabo Ta Gwamnan Shekara 2025 Daga Jaridar The Sun A Legas
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo ta Gwamnan Shekara 2025 daga jaridar The Sun, bisa la’akari da irin nasarorin da ya samu a fannin shugabanci da gudanar da mulki.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu a ranar Lahadi.
- 2023: Matsin Lamba Ba Za Ta Sa Na Janye Takarata Ba – A.A Zaura
- Yanzu-yanzu: Mahaifiyar A.A. Zaura Ta Shaki Iskar ‘Yanci
An miƙa lambar yabon ne a wani biki da aka gudanar a Eko Hotels, Jihar Legas, inda Sanata Orji Uzor Kalu ya gabatar da kyautar, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
An karɓi lambar yabon a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun Alhaji Abdulkareem A. Zaura (A.A. Zaura). A wajen bikin, an kuma karrama wasu gwamnonin jihohin Zamfara da Cross River.
Haka kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya samu lambar yabo ta Sanatan Jin-ƙai na Shekara.
Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, A.A. Zaura ya bayyana cewa wannan karramawa wata babbar ƙarfafa guiwa ce ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ƙara ƙaimi wajen samar da ingantaccen mulki ga al’ummar Jihar Kano. Ya ce wannan yabo bai zo da mamaki ba, duba da yadda gwamnan ya kasance ɗaya daga cikin gwamnonin da aka fi yaba wa a ‘yan kwanakin nan, sakamakon manufofinsa na jin daɗin al’umma da ayyukan da ake gani a fili.
Ya tunatar da cewa a shekarar 2025 kaɗai, Gwamna Yusuf ya samu lambobin yabo guda biyar da suka shafi ilimi, ciki har da ta Gwamnan da Ke Kaunar Malamai daga Ƙungiyar Malaman Nijeriya (NUT), da kuma yabo daga jaridun LEADERSHIP, Blueprint da New Telegraph.
A cewarsa, an kuma karrama gwamnan da lambobin Gwamnan Da Ke Son Ma’aikata da Gwamnan Da Ke Son Tsofaffin Ma’aikata, bayan biyan sama da Naira biliyan 27 na bashin fansho da garatuti.

Zaura ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi a matsayin gwamna na farko da ya aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 71,000, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen kare walwalar ma’aikata.
Cikin tawagar da ta halarci bikin akwai tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba da tsohon Shugaban Ma’aikatan Jiha, Usman Bala da Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Yaɗa Labarai, Ibrahim Adam da Darakta Janar, Asma’u Jibril da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sadaukar da wannan lambar yabo ga al’ummar Jihar Kano, bisa ga goyon baya, haɗin kai da addu’o’in da suke masa. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da ƙarin ribar dimokiraɗiyya tare da hanzarta bunƙasar jihar baki ɗaya.
[ad_2]
Source link