Taron Masu Ruwa da Tsaki na Arewa maso Yamma Zai Zama Hanyar Bunkasa Yankin — Shettima

[ad_1]

Jigo a jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, Ambasada Usman Yerima Shettima, ya bayyana taron masu ruwa da tsaki na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna a matsayin wata muhimmiyar hanya da za ta taimaka wajen ciyar da yankin gaba da kuma magance dimbin ƙalubalen da ke addabar yankin.

Honarabul Yerima ya ce, duba da irin matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewa da yankin Arewa maso Yamma ke fuskanta, babu shakka irin wannan taro zai taimaka matuƙa wajen kawo ƙarshen matsalolin da suka daɗe suna hana yankin samun ci gaba.

  • Shugabar Bulgaria Iliana Yotova: Muna Begen Ganin Kamfanonin Sin Sun Kara Zuba Jari A Kasarmu
  • Yadda Ake Hada Dilka Na Amare

Shettima Yerima ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala bude taron. Ya ce taron ya haɗa kowane bangare na al’umma, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba, domin tsara ingantacciyar hanya ta samun ci gaban tattalin arziki da siyasa a yankin.

A cewarsa, a matsayinsu na mahalarta taron, sun shirya tsaf domin gabatar da muhimman batutuwan ci gaba da suka shafi farfaɗo da masana’antu da suka durƙushe, rage matsalar rashin tsaro ga rayuka da dukiyoyi, bunƙasa harkar noma ta zama sana’ar dogon lokaci, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin kabilu da addinai daban-daban a Arewa baki ɗaya.

Honarabul Yerima ya ƙara da cewa shugabannin Arewa, duk da bambancin ra’ayoyin siyasa, za su haɗa kai wajen jagorantar samar da taswirar hanyoyin magance matsaloli da suka daɗe suna hana yankin samun ci gaba a baya, tare da buɗe sabon babi na cin gajiyar dimbin albarkatun ɗan Adam da na ƙasa da yankin ke da su.

Ya kuma yi wa mahalarta taron daga jihohi bakwai na Arewa maso Yamma fatan samun tattaunawa mai armashi wadda za ta amfani yankin da ma sauran shiyyoyin ƙasar nan.

A ƙarshe, Shettima Yerima ya yi kira ga masu shirya taron hukumar raya Arewa maso yamma (NWDC), Kwamitin Majalisar Dattawa kan Arewa maso Yamma, da gwamnonin jihohi bakwai na yankin da su tabbatar da aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron, domin amfanin al’ummar Arewa maso Yamma baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *