Kotu ta rushe shugabancin PDP ƙarƙashin Tanimu Turaki
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Tarayya a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, ta soke shugabancin jam’iyyar PDP ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Uche Agomoh, ta kuma dakatar da babban taron jam’iyyar da ake shirin yi.
Hakazalika, kotun ta amince da ɓangaren shugabancin riƙon kwarya na Mohammed Abdulrahman a matsayin sahihin shugabancin jam’iyyar na wucin-gadi, har sai an gudanar da babban taron jam’iyyar.
Rahotanni sun ce wannan ɓangare na samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Sai dai ɓangaren Tanimu Turaki, ya ce ba zai amince da hukuncin ba, kuma zai ɗaukaka ƙara.
Kakakin kwamitin zartarwa na jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce sun tuntuɓi lauyoyinsu domin ɗaukar matakan da suka dace.
Ya kuma ce a ganinsu, ɓangaren Turaki ne har yanzu ke da sahihin shugabanci a jam’iyyar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link