AKCILS Ta Karrama LEADERSHIP HAUSA Da Lambar Yabo Ta Gwarzuwar Jaridar Hausa Ta Yanar Gizo Ta Shekarar 2025

[ad_1]

Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano (AKCILS-Legal) ta karrama Jaridar LEADERSHIP HAUSA (Online) da kyautar girmamawa ta “Gwarzuwar Jaridar Hausa ta Shekarar 2025” a ɓangaren kafar yanar gizo da shafukan sada zumunta.

An bayar da kyautar ne bisa rawar da jaridar take takawa wajen yaɗa labarai da rahotanni cikin harshen Hausa mai inganci, tare da bunkasa harshe da al’adu da adabin Hausa ta hanyar kafafen yada labarai na zamani.

  • Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
  • Za A Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Na Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Birnin Beijing

An gabatar da shaidar karramawar a yayin Bikin Makon Hausa na Shekarar 2025, wanda Kwalejin ta shirya kuma aka gudanar da shi a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Janairu, 2026, mai taken baje-kolin al’adun Bahaushe. An mika kyautar ne a ranar Alhamis, 29 ga Janairu, a Dakin Taro na Haruna Bashir da ke harabar Kwalejin.

Mataimakin Shugaban Kwalejin, Dakta Ali Tamasi Mu’az, ne ya mika kyautar a madadin Sashen Hausa na Kwalejin ga Hukumar Gudanarwar Jaridar LEADERSHIP wanda Shugaban Sashen Hausa na LEADERSHIP a bangaren yanar gizo, Muhammad Bashir Amin, ya karɓi kyautar a madadin jaridar.

LEADERSHIP HAUSA

A yayin gudanar da shagulgulan Bikin Makon Hausa, an gudanar da baje-kolin al’adun Hausawa, da kaɗe-kaɗe da raye-raye, tare da karrama wasu kafafen yaɗa labarai na Hausa da malamai da suka kammala karatun digiri na uku da wasu kamfanoni da kuma wasu fitattun mutane da suka ba da gudummawa wajen bunƙasa harshen Hausa.

Daga cikin manya mahalarta taron akwai Farfesa Abdulkadir Dangambo, da Barwan Kano daga Masarautar Kano, tare da sauran shugabanni da malamai da ɗalibai daga sassa daban-daban.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *