An kama abubuwan fashewa 954 da ake shirin kai wa ’yan ta’adda Zamfara




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama mota da ke ɗauke da abubuwan fashewa guda 954 da ake zargin ana shirin kai su ga ’yan ta’adda da ke jihar don hada bama-bamai.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce an kuma kama direban motar mai suna Mustapha Mohammad.

Abubakar ya ce jami’an rundunar na musamman kan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne suka gudanar da wannan samame bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewarsa: “A ranar 27 ga watan Janairu, 2027, da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, jami’an yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, ƙarƙashin jagorancin ASP Aminu Aliyu, bisa sahihan bayanai, sun gudanar da samame wanda ya kai ga kama wani mutum da ake zargi da mallakar boma-bomai ba bisa ka’ida ba.”

“An kama wanda ake zargin, mai shekaru 38, yana tukin motar Toyota Corolla mai lambar rajista KUJ 933 EJ. Binciken motar ya kai ga gano abubuwa 954 da aka ɓoye cikin buhunan roba.

“Binciken farko ya nuna cewa an shirya amfani da kayan wajen kera boma-boman da ’yan ta’addan ke amfani da su,” in ji Kakakin.

Abubakar ya ce wanda ake zargin yanzu haka yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da aka mika kayan da aka kama ga sashen kula da bama-bamai na rundunar domin ajiyewa da ƙarin bincike.

Ya ƙara da cewa bincike na ci gaba don gano asalin kayan, inda aka nufa da su, da kuma gano duk wani abokin haɗin gwiwarsu.

Ya ce: “Za a ci gaba da sanar da sakamakon binciken a yayin da yake ci gaba da tafiya.”

Kamun dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan irin wannan lamarin a Jihar Oyo, inda jami’an ‘yan sanda suka dakatar da babbar mota mai ɗauke da kayan da ake zargin sassan bama-bamai ne a yankin Saki na Oke-Ogun.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *