Gwarzon 2025: Malamin Firamare Ya Samu Kyautar N50m Da Sabon Gida

[ad_1]

Malamin makarantar firamare, Solanke Francis Taiwo, ya samu lambar yabo a matsayin gwarzon malami na shekarar da ta gabata.

An ba shi kyautar Naira miliyan 50, sabuwar mota da kuma gida mai ɗakuna biyu a matsayin gwarzon malami na shekarar 2025 a Nijeriya.

  • Zhao Leji Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Senegal
  • Gwamna Yusuf Zai Yi Nadamar Barinmu – Kwankwaso

Baya ga Taiwo, wasu malaman 11 daga jihohi 36 da Abuja su ma sun samu kyautar Naira miliyan 25 kowanensu saboda irin ƙwazon da suka nuna wajen koyar da yara da kuma kula da tarbiyyarsu.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wannan shiri na karrama malaman don nuna godiya ga irin rawar da suke takawa wajen ilimantar da yara da kuma tarbiyyarsu.

Kyaututtukan sun kai jimillar Naira miliyan 325 a bikin da aka gudanar a Abuja.

Solanke yana koyarwa a makarantar Ansar-ud-Deen da ke Abeokuta, a Jihar Ogun.

Sauran malaman da suka samu kyauta sun haɗa da David Kachollom Joseph daga Filato, Malam Musa Abubakar Garba daga Kaduna, Ifetike Hope Chukwube daga Anambra, Obafemi Peter Lawal daga Legas, Johanna Gilando, Bashar Hantsi daga Kebbi, Blessing Ikong, Chinwe Ituma, Gambo Lawan, Khadijat Galadima da Okide Ochike.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *