Gwamna Yusuf Zai Yi Nadamar Barinmu – Kwankwaso
[ad_1]
Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa kuma shugaban Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce yana da yaƙinin cewa, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da makusantan sa za su yi nadamar barin NNPP daga baya.
Kwankwaso ya ce, ficewar Gwamna Abba daga NNPP ta zo wa mutane da yawa mamaki, ya kara da cewa shi ma da farko ya ji kamar mafarki ne.
“Mutane da yawa da na yi magana da su, sun ji kamar wani irin shiri ne – tsakanina da shi, ko tsakaninsa da wasu. Har ma sau da yawa, ina ganin abubuwan kamar a mafarki,” in ji Kwankwaso.
A ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, Gwamnan Jihar Kano ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC, bayan ya sanar da yin murabus daga NNPP a ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, ƙasa da shekaru uku bayan lashe zaben gwamnan Kano.
[ad_2]
Source link