Mahaifin Wilfred Ndidi Ya Rasu

[ad_1]

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles) Wilfred Ndidi ya rasa mahaifinsa, Sunday Ndidi, a wani hatsarin mota da ya rutsa dashi a jihar Delta yau Talata, an ruwaito cewa tsohon jami’in soja mai ritaya ya gamu da ajalinsa a wani hatsarin mota da ya faru a Umunede, inda aka tabbatar da mutuwarsa jim kadan bayan an garzaya da shi wani asibiti dake Agbor.

Kungiyar kwallon kafa ta Besiktar inda Ndidi ke taka leda ta sanar da faruwar lamarin, inda ta jajantawa dan wasan nata akan wannan babban rashi na mahaifi, a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na X ta bayyana cewar “Munyi matukar bakin ciki da jin labarin rasuwar mahaifin dan wasan kwallon kafa Wilfred Ndidi, Sunday Ndidi, a wani hatsarin mota mai muni,”.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “Muna fata Allah ya jikan mamacin, sannan muna mika ta’aziyyarmu ga dan wasan kwallon kafa Wilfred Ndidi, iyalansa, da kuma masoyansa”, kwanan nan Ndidi ya jagoranci Nijeriya a wasannin cin kofin kasashen nahiyar Afirika da aka kammala a kasar Morocco, inda Nijeriya ta kare a matsayi na uku, hakazalika Ndidi ya zura kwallonsa ta farko tun bayan fara bugawa Nijeriya wasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *