Sauya Sheƙar Gwamnan Kano Zuwa APC Cin Amana Ne – NNPP
[ad_1]
Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta ce sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC cin amana ne ga jam’iyyar, jagoranta Sanata Rabiu Kwankwaso, da kuma al’ummar Kano.
Kakakin NNPP, Ladipo Johnson, ya ce jam’iyyar ba ta da ƙarfi sosai a Kano kafin zaɓen 2023, amma ta samu nasara ne saboda tasirin Kwankwaso da goyon bayan jama’a.
- Sheikh Joaan Ya Zama Sabon Shugaban Kwamitin Olympics Na Yankin Asiya
- Shugaban Kasar Uruguay Yamandu Orsi Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Ya ce mutane sun yi tsayin daka wajen mara wa Abba Kabir Yusuf baya har zuwa Kotun Ƙoli, don haka ya kamata a ce an tuntuɓe su kafin ɗaukar wannan mataki.
Wani jami’in jam’iyyar, Ibrahim Karaye, ya ce NNPP ta yi matuƙar takaici da abin da ya faru, amma har yanzu jam’iyyar na da ƙarfi a Kano kuma tana da ƙwarin gwiwar ci gaba da samun goyon bayan jama’a.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC a hukumance tare da ‘yan majalisar dokokin jihar 22 da kuma ‘yan majalisar tarayya tara.
A wajen taron komawarsa APC, Abba ya ce ya yi shawara da mutane da dama kafin ɗaukar matakin, kuma ya ce hakan yana da nufin amfanar da Jihar Kano.
Ya ƙara da cewa komawarsa APC zai ba shi damar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya domin kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaban Kano.
[ad_2]
Source link