Ƴan Majalisar APC Na Binuwe Sun Sha Alwashin Ƙuri’u Miliyan 1 Ga Tinubu A 2027
[ad_1]
Tawagar jam’iyyar APC ta jihar Binuwe a Majalisar Tarayya ta bayyana aniyarta na tabbatar da ƙarin ƙuri’u miliyan ɗaya ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda ta danganta wannan shiri da aikin yin rajistar intanet (e-registration) da sabunta rajistar mambobi domin faɗaɗa tushen jam’iyyar a faɗin jihar.
Hon. Philip Agbese, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ado/Okpokwu/Ogbadibo kuma kakakin tawagar APC ta Binuwe a Majalisa, ya bayyana hakan a Makurdi. Ya ce matakin na daga cikin shirin haɗa ƙarfi da ƙarfe da manyan jiga-jigan jam’iyyar, musamman ta hanyar aiki tare da wata kungiya ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, domin tabbatar da cewa mambobin jam’iyyar da aka tantance sun shiga cikin tsarin rajistar na intanet.
- Sojoji Sun Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Kayayyakin Gwamnati A Binuwe
- Sarkin Musulmi Ya Nuna Baƙin Ciki Kan Kisan Kiyashi A Binuwe
Agbese ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa haɗa tsarin Akume da aikin rajistar zai ƙara yawan mambobin APC a Binuwe sosai. “Ƙungiyar Akume kaɗai na da mambobi fiye da rabin miliyan da aka tantance, kuma a cikin kwanaki bakwai masu zuwa za mu shigar da dukkan sunayensu. Wannan zai ƙara yawan mambobin APC da aƙalla 500,000, kuma muna nufin samun ƙarin ƙuri’u miliyan ɗaya ga Shugaba Tinubu a zagayen zaɓe na gaba,” in ji shi.
Ya yi kira ga mambobin APC a faɗin jihar da su ba da cikakken haɗin kai ga jami’an jam’iyya a matakin ƙananan hukumomi domin tabbatar da nasarar aikin rajistar, yana mai gargaɗi kan rarrabuwar kai da sakaci. Ya jaddada cewa jam’iyyar za ta mai da goyon bayan jama’a zuwa gagarumar nasarar zaɓe a 2027, tare da cewa APC a Benue na shirin dawowa da ƙarfi fiye da da.
[ad_2]
Source link