Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Fashi da Makami A Abuja, Sun Kama Wani Mutum
[ad_1]
Rundunar ƴansandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta daƙile wani yunƙurin fashi da makami a yankin Kado na Abuja, inda ta kama mutum ɗaya tare da ƙwato makamai da wasu kayayyakin da ake zargi na masu laifi.
A wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Litinin, ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026. Ta bayyana cewa ofishin ƴansanda na Mabushi ya samu kiran gaggawa cewa ƴan fashi na kai wa direbobi hari a kusa da gidan mai na MRS da ke Kado, lamarin da ya sa ƴansanda suka gaggauta kai ɗauki.
- Hukumar FCTA Ta Fatattaki Mabarata 607 Daga Titunan Abuja
- Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
Adeh ta ce da zarar jami’an suka isa wurin, waɗanda ake zargin su kusan uku ne, sun yi ƙoƙarin tserewa bayan sun hango ƴansanda, abin da ya haifar da artabu da musayar harbe-harbe. “A yayin wannan artabu, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ya samu raunin harbin bindiga kuma aka kai shi asibiti domin jinya, yayin da sauran suka tsere zuwa dazuka da ke kusa,” in ji sanarwar.
Ƴansanda sun tabbatar da cewa sun ƙwato abubuwa da dama daga wurin, ciki har da motar da ake zargin masu laifin ke amfani da ita. Daga cikin kayan da aka samu akwai mota kirar Volkswagen Golf 2 mai launin baƙi mai lambar rajista JJJ 112 DWda bindigar Barreta guda daya, da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, da janareta ƙirar Firman, da wayoyin hannu biyu, da katin ATM na Access Bank, da wasu kayayyaki kamar danƙon harbi (catapult), fensir na karfe (pliers), takalma, huluna da wasu kayan sawa.
Ta kara da cewa rundunar na ci gaba da farautar sauran wadanda suka tsere, tare da tabbatar da kudurin Kwamishinan ’Yan Sanda na FCT, CP Miller G. Dantawaye, na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar babban birnin. Haka kuma, ’yan sanda sun bukaci mazauna Abuja da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani abu da suka ga yana da shakku ta hanyar layukan gaggawa na rundunar.
[ad_2]
Source link