Yau ake sa rana Abba zai koma APC

[ad_1]



A Litinin ɗin nan ake da ran Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sanar da sauya sheƙarsa zuwa Jami’ar APC, bayan a ranar Juma’a ya sanar ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ficewarsa daga NNPP tare da ɗauƙacin shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 da ’yan majalisar dokokin jihar 23 da ’yan majalisar to Tarayya takwas.

Gwamnan wanda aka jima ana ce-ce-ku-ce game da shirin komawarsa APC, ya alaƙanta ficewarsa daga NNPP da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.

Ficewar Gwamna Abba daga NNPP wadda ake alaƙantawa da tsamin dangantaka tsakaninsa da uban gidansa na siyasa, tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Abba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *